Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bazoum Ya Jaddada Aniyarsa Ta Kama Masu Barnata Dukiyar Kasa


Shugaban Jamhuriyar Nijer, Mohamed Bazoum.
Shugaban Jamhuriyar Nijer, Mohamed Bazoum.

Shugaban kasar Nijar ya ba da umarnin daukar duk matakan da suka dace don magance matsalar da ke faruwa a hukumar shige da fice da kuma ma’aikatar haraji ta kasar.

A yayin bukin taya murnar shiga sabuwar shekarar mai ladiya ta 2023 da ya gudana a karshen mako wanda ya sami halartar manyan jami’an da suka hada da fara minista da mambobin gwamnatinsa da shugaban Majalissar Dokokin kasa da shugabannin tsaro, shugaba Mohamed Bazoum ya jaddada aniyar yaki da cin hanci da farautar barayin dukiyar jama’a.

Shugaba Bazoum ya ce hukumar HALCIA ta damka wa alkali mai shigar da kara rahoton binciken badakala da masu yawa, hakan ya sa ya ba da umurnin bin diddigin batun ta hanyar bincike.

Haka kuma shugaban ya kara nanata kira ga alkalan shari’a su yi aiki kamar yadda doka ta tsara, domin aikinsu na da mahimmanci sosai a yaki da masu aikata laifuka. Sannan ya zama wajibi su kiyaye goyon bayan takwarorinsu da aka yi katarin samu da aikata abin da ke zubar mutunci alkalanci.

Shugaban kasa wanda ya tunatar da cewa ba a taba kama manyan jami’an gwamnati ba a Nijer tun daga samun ‘yancin kai, kamar yadda ya ke yi a zamanin mulkinsa ya kudiri aniyar saka kafar wando guda da baragurbin jami’an douane da na ma’aikatar haraji.

Har yanzu akwai sauran rina akan maganar tattara kudaden kasa da harakokin hada hada lamarin da ake dora alhakinsa a wuyan ma’aikatar Douane da ta haraji kamar yadda ake iya ganewa daga korafe korafen da masu saka hannun jari ke yi akan su.

Da farko na dauki wannan magana a matsayin kage to amma da alama batun na bukatar dubawa sosai, saboda haka ya umarci fara minista da ministan kudi da su dauki matakan da suka dace.

Shugaban reshen transaparecy Nijer Malan Maman Wada ya bayyana fatan ganin dorewar wannan yunkuri. Tare da yabawa gwamnati game da tashi tsaye don warware wannan matsala.

A cewar shugaban kungiyar Voix des Sans Voix Nassirou Saidou, a yanzu hankulan ‘yan kasa sun karkata wajen alkalan shara’a da hukumar yaki da cin hanci ta kasa.

Shugaba Mohamed Bazoum ya yi wannan ikirari ne a dai dai lokacin da bincike ya rutsa da wani alkali da ake zargi da rubda ciki akan gomman miliyon cfa na kudaden gado, ba’idin wasu da aka gano suna karbar na goro don bada belin gaggan ‘yan takife yayin da aka cafke babban darektan wata makarantar gwamnati da wasu mukarrabansa saboda zargin cuwa cuwar jarabawa kamar yadda babban darektan bankin BAGRI da mataimakansa ke kulle a gidan kaso sanadiyar zargin halitta dubban miliyoyin cfa da suka wawure.

Saurari rahotan Sule Muminu Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

XS
SM
MD
LG