Hukumomi A Jamhuriyar Nijer Sun Kara Kaimi A Yaki Da COVID-19

Shugaban Kasar Jamhuriyar Nijer

Hukumomin kiwon lafiya a jamhuriyar Nijer sun bayyana shirin kara tsaurara matakan dakile annobar COVID-19 bayan da aka gano wasu mutane da dama da suka harbu da kwayar cutar a makon jiya, saboda haka aka gargadi jama’a a kan maganar mutunta ka’idodin kare kai daga wannan anoba.

Daga farkon watan Nuwamban da muke ciki kawo yanzu yawan wadanda suka kamu da cutar coronavirus a Nijer ya karu daga mutane 11 zuwa 84 a karshen makon jiya, lamarin da hukumomin kiwon lafiyar al’umma ke dangantawa da yanayin da ake ciki a kasashen waje inda a yanzu haka annobar ke kara muni.

Hakan ne kuma yasa hukumomi suka kaddamar da yunkurin tsaurara matakai a filayen jragen sama kamar yadda sakataren ofishin ministan kiwon lafiya kuma mamba a kwamiti yaki da cutar corona Abache Ranaou ya bayyana a taron manema labarai.

Sake kunno kai da cutar ta yi a karo na biyu, ta zo da tsanani har ma wasu kasashen duniya basu san irin matakan da zasu dauka wurin dakile cutar ba. Ya ce yanda mutane ke kamuwa da cutar, dalili kenan da yasa gwamnati take sa ido sosai a kan masu shiga kasar ta filayen saukar jiragen sama.

Rashin mutunta ka’idodin kariya a nan cikin gida ma wani abu ne da ake ganin zai iya maida hannun agogo baya a yaki da cutar coronavirus a wannan kasa musamman a wannan lokaci na shigar yanayin sanyin hunturu sabili kenan mahukunta ke jan hankulan jama’a akai.

Ranaou, ya ce da ma can yanayin sanyi na zuwa da cututtuka da dama, kamar ciwon kai da masassara da majina da sauran alamomi masu kama da cutar coronavirus, saboda haka ne yasa gwamnati ta bukaci mu tashi haikan mu wayar da jama’a tun abubuwa basu sha karfin mahukunta ba.

Ya ce mutane suna yin watsi da matakan da gwamnati ta dauka a wannan yaki da cutar, kamar sanya kyallen rufe huska da hana yin taron jama’a da yawa da wanke hannu da ruwa da sabulu alhali kuma cutar na karuwa a cikin kasar.

A ranar 19 ga watan Maris wannan shekara ne aka gano mutun na farko da ya harbu da cutar coronavirus a jamhuriyar Nijer lamarin da ya sa hukumomi kafa dokar takaita zirga zirga da cudanyar jama’a da rufe makarantu da wuraren ibada da na shakatawa da filayen jiragen sama da tashoshin motoci kafin daga bisani a sasauta.

Toh sai dai lura da yadda yawan wadanda suka kamu da wannan cuta a ‘yan kwanakin nan ke kara cirawa sama ya sa hukumomin kiwon lafiya soma yunkurin kara jan damara domin tunkarar wannan

Ga dai rahoton da Souley Moumouni Barma ya aiko mana:

Your browser doesn’t support HTML5

KARFAFA MATAKAN YAKI DA COVID 19 A NJIJER