Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Ta'adda Na Kawo Tsaiko Ga Zaben Burkina Faso Na Wannan Wata


Shugaban Burkina Faso, Roch Marc Christian Kabore
Shugaban Burkina Faso, Roch Marc Christian Kabore

Reshen kungiyar IS a yankin Sahel ta fada a jiya Asabar cewa ta kaddamar da wani harin kwantan bauna na tsakiyar mako da ya hallaka sojoji 14 a kasar Burkina Faso mai mayakan jihadi kafin zaben kasar na wannan wata.

Kungiyar mayakan jihadin ta ce itace ta kaddamar da wannan hari, daya daga cikin mununan hare hare a kan sojoji, a wani sako da ta kafe a shafin labaran kungiyar na Amaq da kuma shafukan labarai na zamani.

Kungiyar ta ce ta kashe sojoji ashirin a cikiin wani ayari dake kan hanyarsa a Tin Akoff a lardin Oudalan a ranar Laraba.

A ranar Juma’a, wata kungiyar ‘yan bindiga mai hamayya ta GSIM, itama ta dauki alhakin kai hari a kan shafukanta na sada zumunta.

Wani mai magana da yawun gwamnati ya fada a ranar Alhamis cewa mutum 14 ne suka mutu, yayin da yake dora laifin kai harin a kan kungiyoyin ‘yan ta’adda.

An kai harin ne a arewacin kasar, kusa da iyakarta da kasar Mali da Nijer kana harin na zuwa ne kwanaki kalilan kafin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki da za a yi a ranar 22 ga watan Nuwamba.

Tashe tashen hankula na baya bayan nan, yasa ‘yan takara da dama, ciki har da shugaban kasa mai ci, Roch Marc Christian Kabore, sun dakatar da gangamin yakin neman zabensu na kwanaki biyu.

Tashin hankalin zai hana sama da kauyuka dubu daya da dari biyar a cikin kauyuka dubu takwas na kasar damar yin zabe.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG