Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fiye Da Mutane 170,000 Suka Kamu Da COVID-19 a Rana Guda a Amurka


Jami'an gwaje-gwajen COVID-19
Jami'an gwaje-gwajen COVID-19

Amurka ta kara sumun adadin tarihi na masu kamuwa da coronavirus a rana guda.

Sama da mutane 170,000 ne aka samu rahoton sun kamu da cutar a ranar Juma’a 13 ga watan Nuwamba a cewar shirin da ke bin diddigin bayanan COVID-19 da cibiyar samar da bayanan jami’ar Johns Hopkins, karin kusan mutun 20,000 daga shekaranjiya Alhamis, yayin da jihohin kasar suka bada rahoton an yi gwaje-gwaje miliyan 1.7.

Mutane kusan miliyan 10.74 ne suka kamu da coronavirus a Amurka, fiye da kowacce kasa. Haka kuma Amurka ce ke kan gaba a duniya a adadin mace-mace inda ta samu mace-mace 244,357 ya zuwa safiyar Asabar 14 ga watan Nuwamba, ciki har da mace-mace 1,3000 cikin sa’o’i 24 da suka gabata.

Alkaluman shirin da ke bin diddigin bayanan COVID-19 sun nuna cewa mutane fiye da 69,000 aka kwantar asibiti sakamakon COVID-19, karin kusan mutane 2,000 kwana daya kafin ranar.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG