A ta bakin jami’in hukumar zaben Ahmed Bello, hukumar ta dukufa wajen samarwa da ‘yan Najeriya nagartaccen zabe a shekarar 2019 idan Allah ya kaimu.
Yanzu haka dai a fakaice manyan jam’iyyun Najeriya sun fara kamfen din zabe mai zuwa. Jam’iyyar APC mai mulki ta yi watsi da zargin da PDP ta yi, cewa akwai shirin murde zaben na 2019. PDP dai har ta bukaci sa bakin hukumomi na kasa da kasa kan fargabar.
Shugaban aikin tsare kuri’a na Buhari, Kailani Mohammad, ya ce tamkar PDP ta ankarar da su ne, duk kuwa da irin matakan da za a dauka don tabbatar da sahihancin zabe, dole ne su saka ido daga farkon zaben har karshe.
Shi kuma kakakin shugaban PDP, Shehu Yusufu Kura, cewa yayi zasu ‘dauki matakan hana duk wani nau’i na magudi. Kuma yayi kira ga jam’iyyar APC da yi abin da jam’iyyar PDP ta yi na gudanar da zabe iriin wandan PDP ta yi kuma duniya ta amince da shi.
Gabanin nasararsa a zaben 2015 shugaba Buhari ya je kotu da PDP har sau uku tun 2003, inda da ya lashe zabe a karo na farko ya ce kuri’ar mutane ta yi aiki, wanda ba mamaki amincewa da shan kaye ne ya hana tsohon shugaba Jonathan kalubalantar zaben a kotu.
Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5