A cigaba da kaddamar da ayyukan cigaba da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke yi, yau ya isa birnin Ikko, inda ya kaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin jahar karkashin gwamna Akinyomi Ambode ta yi baya kuma ga aza harsashin gina wata babbar tashar jirgin ruwa kan biliyoyin daloli, da zummar rage cinkoso a tashar jirgin ruwan Lagos.
Da ya ke kaddamar da babbar tashar motocin haya, Shugaba Buhari ya ce, “Na jinjina ma gwamnan jahar saboda ayyukan da ya yi cikin shekaru uku kawai.” Kamar tashar jirgin ruwan da ake shirin fara ginawa, ita ma sabuwar tashar motocin hayar an gina ta ne saboda a rage cinkoson motoci a titunan birnin, wanda ake kuma sa ran hakan zai taimaka ma matafiyan da ke yawan shiga da fita wannan babban birni kuma cibiyar kasuwancin Najeriya.
Shugaba Buhari ya kuma halarci wani taron da aka shirya na tunawa da shekaru 66 da haihuwar babban jagoran jam’iyyarsu ta APC, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, wanda ake kuma yi wa kirari jagaban Bargu. Tuni dai talakawa a Ikko su ka fara bayyana ra’ayoyinsu kan wannan siyara da Shugaba Buhari. Su masu nuna farin cikinsu da ziyarar da kuma yin addu’a ma Shugaba Buhari. Saidai wani dan arewa da ya ce ya na fama da matsalar kudi, ya ce ko a jikinsa wannan ziyarar.
Tuni aka fara cece-kuce da kuma danganta ziyarar da farfagandar siyasa a yayin da wasu kuma ke jadda alfanunta ga jahar da kuma kasar baki daya.
Ga wakilinmu Babangida Jibrin da cikakken rahoton:
Facebook Forum