Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Su Dino: An Kasa Kamo ‘Yan Bindigar da Su Ka Tsere


Wasu 'yansandan Najeriya a bakin aiki
Wasu 'yansandan Najeriya a bakin aiki

Tana kasa ta na dabo game da batun farauto 'yan bindigar nan shida da su ka bace bat yayin da su ke tsare hannun 'yansandan jahar Kogi saboda wani rikici mai nasaba da Sanata Dino Melaye.

Har yanzu ‘yansanda sun kasa kamo ‘yan bindigar nan guda shida da aka ce wai sun tsere yayin da su ke tsare a caji’ofis din ‘yansanda a jahar Kogi a ranar Larabar da ta gabata. Idan an tuna dai a ranar Labarar nan da ta gabata ne Mataimakin Shugaban ‘Yansanda mai kiula da shiyya ta takwas, wadda ta kunshi jahohin Kogi, Ekiti da kuma Kwara, AIG Jibrin Yakubu ya ce sun baza jami’ansu tare da hotunan ‘yan bindigar da su ka tsere din a sassan Najeriya kuma su na da kwarin gwiwar cewa nan ba da jimawa ba za a sami nasarar kama su.

Da ya ke bayani ma wakilin Sashin Hausa da ke Minna, Mustapha Batsari, Mataimakin Shugaban ‘Yansandan ya suna kira ga ‘yan kasa baki daya da su zuba ida, muddun su ka gano su to su bayar da rahoto don a damko su.

Yayin da ake jiran a ga yadda za ta kaya, mutane a jahar ta Kogi da ma kasar baki daya na cigaba da cece kucen yadda yadda aka yi mutanen da ake zargi da aikata babban laifi haka su ka sulale yayin da ake tsare da su.

Ga wakilinmu Mustapha Batsari da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG