Hukumar DSS ta ce dalilin tayar da rikicin shi ne a ingiza ‘yan Najeriya su afka wa junansu, a irin tarzomar kabilanci ko ta banbancin addini.
A wata sanarwa da hedikwatar hukumar tsaron DSS ta fitar, ta gargadin masu shirin tayar da fitinar da su yi wa kansu fada, idan ba haka ba zasu iya fuskantar fushin hukumar.
Wannan gargadi shi ne karo na biyu cikin makonni biyu da hukumar DSS ta fitar, inda a baya ta yi gargadin cewa ta bankado shirin da wasu ke yi da sa hannun wasu ‘yan kasashen waje, domin haddasa rudami a Najeriya.
Masana tsaro na kallon wannan gargadi da cewa abu ne a bayyane karara, ganin yadda wasu ‘yan Najeriya da ke zaune a kasar ko kasashen Turai, ke yada hotunan bidiyo da wasu rubuce-rubuce ta kafafen sada zumunta.
Kwararre a fannin tsaro Faruk Bibi Faruk, na jami’ar Abuja, ya bayyana damuwarsa kan yadda gwamnatin Najeriya ba ta daukar mataki ta hanyar kiran jakadun kasashen wajen da mazaunansu ke aikata laifukan yada labaran karya, domin yi musu gargadi.
Domin cikakken bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.
Your browser doesn’t support HTML5