Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Arewacin Najeriya Ke Ci Gaba Da Fuskantar Matsalar Tsaro


Al'ummomi a Arewacin Najeriya na ci gaba da fuskantar hare-haren 'yan ta'adda duk da matakan da gwamnatoci ke cewa suna dauka.

Ko a karshen wannan mako kananan hukumomi uku a Gabashin Sakkwato sun fuskanci wadannan matsalolin na hare-hare.

Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal
Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal

A karamar hukumar Goronyo maharan sun yi dirar mikiya a garin Shinaka inda suka harbi mutane masu yawa har an samu daya daga cikinsu ya rasu.

Haka kuma a karamar hukumar Rabah maharan sun dira a garin Kogogo Rijiya.

Sannan a Sabon Birni ma garin Tsamaye ya dauki bakuncin barayin.

Duk wadannan suna faruwa ne lokacin da ‘yan sandan al'umma fiye da 360 suke aiki tare da na hukuma don shawo kan wadannan matsalolin.

Sai dai wasu na ganin ko ‘yan sandan hukuma da ke kauyuka ba su iya tunkarar barayin saboda irin makaman da ke garesu.

Wakilin Muryar Amurka ya nemi jin ta bakin rundunar 'yan sanda ta jihar Sakkwato akan wannan batun kuma kakakin rundunar ASP Muhammad Abubakar Sadiq ya ce zai kira shi, amma har zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a ji sa ba.

Gwamnatin Sakkwato daga cikin matakan da tace tana dauka, ta saba yin alwashin samar da wata cibiya da za ta inganta tsaro, a lokacin da gwamnatin ke bayar da motoci ga 'yan sanda .

Bisa ganin cewa yau fiye da wata bakwai da yin wannan alwashin kuma ga ayukkan ta'addanci na ci gaba da wanzuwa muka tuntubi mai ba gwamna shawara akan yada labarai Muhammad Bello ya ce ba’a soma aikin cibiyar ba.

Wannan na daya daga cikin matakai da dama da gwamnatin ta ce za ta dauka kuma ba'a yi ba, wadanda watakila da an aiwatar da su, za su taimaka wajen rage wadannan matsalolin na rashin tsaro, domin yanzu talakawa na ganin ba su da kowa sai Allah zai fitar da su daga wadannan matsalolin na rashin tsaro.

A saurari rahoton Muhammadu Nasir daga Sokoto:

Yadda Arewacin Najeriya Ke Ci Gaba Da Fuskantar Matsalar Tsaro
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG