Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Miyyatti Allah Ta Yi Zargin Cewa An Yi Wa Fulani 87 Kisan Gilla a Jihar Naija


Wasu Fulani
Wasu Fulani

Yayin da ake ci gaba da samun matsalolin tsaro a Najeriya, an shiga zarge zargen juna tsakanin masu ruwa da tsaki.

Da yammacin jiya Alhamis ne aka kammala wani babban taro a tsakanin kungiyar Fulani makiyaya da jami’an tsaro da kuma Gwamnatin Jihar Naija. Taron dai ya mayar da hankali ne akan yadda za a samu bakin zaren matsalar rashin tsaron da ta Addabi jihar da ma jihohin dake Makwabtaka da ita.

A wajen taron, kungiyar Miyatti Allah ta koko akan yadda ta ce wasu jami’an tsaron sa kai sun kutso jihar Naijan daga kasar Zuru ta jihar Kebbi sun hallaka Fulani 87, wadanda ba su san hawa da sauka ba, kamar yadda mataimakin shugaban kungiyar Miyatti Allah a Najeriya, Alh. Hussaini Yusuf Bosso ya yi karin Bayani da cewa irin wannan al’amari ya sa wasu Fulanin sun gudu sun bar Najeriya zuwa kasar Afurka Ta Tsakiya.

Wakilin Gwamnatin jihar Naija a wajen wannan taro Babban Daraktan Harkokin Makiyaya da sulhu a ofishin Gwamnan jihar Naijan, hardo Abdullahi Babaye ya ce Gwamnati tana daukar matakin shawo kan lamarin, kamar yadda yayi karin bayani cewa za a kara tabbatar da tsaro da ganin cewa an samu mai laifi an hukunta shi, amma marar laifi an bar shi. Ya ce mai laifi ma za a masa hukunci ne daidai da laifinsa.

To sai dai rashin halartar Gwamnan jihar Naijan, Alh.Abubakar Sani Bello a wajen wannan taro ya jefa shakku a wajen wasu daga cikin shugabannin Fulanin. Dukkanin wakilan Jami’an tsaro da suka hada da sojoji da ‘yan sanda da kuma na DSS sun bukaci al’ummar Fulanin da su basu hadin kai a yaki da ‘yan ta’adda da kauce wa boye masu laifi.

Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Karin bayani akan: Fulani​, Jihar Naija​, Miyetti Allah Kautal Hore​, Nigeria, da Najeriya.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG