Yadda Aka Harbi Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump A Pennsylvania

Tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump, yayin da halaric taron yakin neman zabe a jihar Pennsylvania

Jami'an bada kariya yayin da suke iskewa da Trump daga filin taron yakin neman zabe

Jami'an leken asiri sun zagaya Trump bayan an ji harbe-harben a filin taron yakin neman zabe

jami'an ba da kariya sun garzaya zuwa wurin Trump kuma an ci gaba da jin karar harbin yayin da jami’an ke kula da Trump.

Dan takarar jam'iyyar Republican, Donald Trump, na gaida magoya bayansa kafin shiga mota

Jami'an leken asiri na shigar da Trump mota yayin da aka garzaya da shi asibiti jinya

Jami'an 'yan sanda sun harbi wanda ya yi harbe harben a lokacin da Trump ke jawabi

Wasu magoya bayan jam'iyyar Republican da suka tsira yayin harbin a filin taron yakin neman zaben Trump

Jami'an tsaro a filin taron yakin neman zabe bayan harin

Filin taron yakin neman zabe a garin Butler na jihar Pennsylvania bayan magoya bayn jam'iyyar Republican sun watse.

An harbi dan takarar jam'iyyar Republican kuma tsohon shugaban Amurka Donald Trump a wani taron yakin neman zabe a garin Butler da ke jihar Pennsylvania a Amurka ranar Asabar.