Biyo bayan yunkurin kashe dan takarar shugaban kasar Amurka na jam’iyyar Republican, Donald Trump, ya yin da yake jawabi a wani gangagmin yakin neman zabe jiya Asabar a garin Butler na jihar Pennsylvania ta Amurka, kwararru a sassan duniya sun shiga fashin baki game da wannan al’amari.
Dr. Faruk Bibi Faruk, na jami’ar Abujan Najeriya ya ce wannan al’amari bai rasa nasaba da al’adar barin kusan kowa ya mallaki bindiga da kuma yadda siyasar Amurka ta fara daukar zafi.
Ya ce ganin yadda ake ma Amurka na jagoriya a fannin dimokaradiyya kuma wacce ke fafutukar yada tsarin siyasar dimokaradiyya a duniya, wannan yinkuri na kashe Tump, wanda ake ganin bai rasa nasaba da siyasa ba, zai yi tasiri kan siyasar Amurka.
Ya ce da an kashe Trump da Allah kawai ya san halin da Amurka za ta shiga.
Ya kara da cewa tunda Trump ya tsallake rijiya da baya, farin jijinsa zai karu a siyasance.
Da aka tambaye shi ko ya na ganin wannan yinkuri na kashe Trump zai yi tasiri kan shirin babban taron da jam’iyyar Republican na gobe Litini da kuma dan takarar da za ta tsayar, wanda ake ganin Trump din ne, yace ‘ga dukkan alamu Trump din ne za a tsayar kuma da wuya jam’iyyar ta yi wani gagarumin sauyi’.
Game da darasin koyo daga wannan al’amari kuwa, Dr Bibi Faruk ya ce ya kamata a daina siyasa gaba, mai cike da zage zage ko mayar da zage zage.
A saurari hirarsa da wakilin Muryar Amurka, Ibrahim Ka-Almasi Garba:
Dandalin Mu Tattauna