Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabbin Bayanai Sun Fito Kan Wanda Ake Zargi Da Harbin Trump


Election 2024 Trump Shooter
Election 2024 Trump Shooter

Wani abokin karatun Thomas Matthew Crooks, matumin da ake zargi da yunkurin kashe Trump, ya bayyana shi a matsayin wanda aka tsangwama, ba mai hulda da shi sosai, yayin da masu bincike suka gano ababen fashewa a cikin motar Crooks da gidansa.

Yayin da masu binciken gwamnatin tarayya ke kokarin gano dalilin da ya sa Thomas Matthew Crooks dan shekaru 20, mutumin da aka bayyana a matsayin wanda ya yi yunkurin kashe tsohon shugaban Amurka Donald Trump, karin tambayoyi suke cin karo da su ba amsoshi ba.

Jami'an hukumar binciken manyan laifuka ta FBI sun yi gargadi a ranar Lahadi cewa, har yanzu binciken na a matakin farko, amma sun ce bayanan da suka samu ya zuwa yanzu sun kasa gano dalilin da ya sa Crooks ya yanke shawarar yin harbin daga saman wani gini a bayan wurin da aka yi gangamin yakin neman zaben.

"Mun samu ‘yan bayanai game da sakonnin da ya tura ta waya da kuma wadanda ya kira ta waya da ya zuwa yanzu basu bayyana wani abu ba dangane da dalilin kai harin ko kuma akwai wani daban da ke hannu a lamarin,” abin da mataimakin daraktan hukumar FBI Paul Abbate ya shaida wa manema labarai kenan.

Wasu jami'ai sun ce da alama Crooks shi kadai ya yi aiki. Kuma sun ce yayin da har yanzu ba su iya bude wayarsa ba, su samu damar ganin abin da ke cikinta, harkokinsa a dandalin sada zumunta ba su nuna yana da wata akida ba.

Discord, dandalin sada zumunta da ya shahara ga masu wasa ta yanar gizo, ya fada a ranar Lahadi cewa ya gano wani shafi "wanda da alama yana da alaka da" Crooks, kuma ga dukkan alama ya karfafa abin da hukumar FBI ke tunani.

"Ba a cika amfani da shafin ba, ba a yi amfani da shi ba cikin watanni da yawa," a cewar wani mai magana da yawun kamfanin Discord a cikin wata sanarwa da ya tura wa Muryar Amurka. "Ba mu ga wata hujja da ke nuna cewa an yi amfani da shafin don kitsa harbin ba, ko neman tada hankali, ko bayyana ra'ayin siyasa."

A halin da ake ciki, wasu da suka san Crooks sun fara magana.

Jason Kohler, ya shaida wa manema labarai ranar Lahadi cewa shi da Crooks makarantar sakandaren Bethel Park a Pennsylvania su ka je, inda ya bayyana shi a matsayin wanda bai cika mu’amulla da mutane ba.

“A lokacin, yaro ne wanda kusan a ko da yaushe za ka ganshi shi kadai. Kuma a ko yaushe ana tsangwamarsa,” abin da Kohler ya fadawa manema labarai kenan a ranar Lahadi. Ya kara da cewa "an kuntata mishi sosai."

A shekarar 2022 ne Crooks ya kammala karatu daga makarantar sakandaren Bethel Park, a cewar wata sanarwa daga gundumar da makarantar ta ke zuwa ga wata kafar yada labarai ta kasar. Rahotanni daga kafafen yada labarai na kasar sun bayyana cewa an taba ba Crooks kyautar dala 500 a fannin lissafi da kimiyya.

Kohler ya ce bai taba yin wata mu'amala sosai da Crooks ba, wanda ya kuma bayyana cewa zai zauna shi kadai a lokacin cin abincin rana kuma sau da yawa wasu yara sukan tsangwame shi saboda yadda ya saba sanya kaya da kuma yadda ya ci gaba da sanya takunkumin rufe hanci da baki har bayan da aka dage dokar sanya shi a lokacin annobar COVID-19.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG