Hukumomin Amurka sun bayyana cewar, Hukumar FBI, mai yaki da manyan laifuffuka a kasar na gudanar da bincike akan yunkurin hallaka tsohon shugaban Amurkan, Donald Trump, a yayin wani taro a jihar Pennsylvania a jiya asabar.
A cewar jami'an binciken FBI mai kula da shiyar Pittsburgh, Kevin Rojek, hukumar bata san dalilin kai harin daya hallaka mutum guda tare da raunata wasu mutane 2 ba.
"Da yammacin yau muka gamu da iftila'in da muka kira da yunkurin hallaka tsohon shugaban kasa Donald Trump. Har yanzu wannan wuri, wuri ne da ba'a kai ga kawo karshen ta'addancin da ake nufin aikatawa ba" a cewar Rojek yayin wata ganawa da manema labarai.
Hukumar ta FBI ta kuma bayyana sunan mutumin da ake zargi da yunƙurin kashe tsohon shugaban Amurkan.
Hukumar ta ce sunan mutumin Thomas Matthew Crooks, kuma ɗan asalin yankin Bethel park ne a Pennysylvania mai shekara 20 da haihuwa.
FBI ta ce tana binciken lamarin a matsayin yunƙurin kisan kai, kuma ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen kammala bincike.
Dandalin Mu Tattauna