Hotuna Daga Sassan Duniya Daban Daban

Jama'a sun taru domin girmama gawar tsohon sakataren majalisar dinkin duniya Kofi Annan a Accra babban birnin kasar Ghana.
 

Jama'a sun yi layi domin sayen iskar Gas a wani shago dake gefen hanya domin shirye shiryen mahaukaciyar guguwa da ake sa ran zata ratsa wani yanki a jihar South Carolina ta kasar Amurka.
 

Dalibai a kasar Indonesia sun yi taro domin murnar sabuwar shekarar musulunci
 

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da na kasar China Xi Jinping, na gaisawa a lokacin ziyarar sa lokacin babban taron tattalin arziki a kasar Rasha.
 

Tankar yaki na harbi yayinda dakarun kasar Koriya ta kudu ke atusaye.

 

Kudan Zuma ya yayyabe jikin wani uutum  Tabu dake kasar Saudiyya
 

'ya'yan masunta na wasa akan ginin wani makewayi da ruwa ya mamaye a kusa da gabar kogi a kasar Indiya.
 

Shaho ya kama dan kaza a gabashin kasar Jamus.

 

Kalli hotuna dake nuna halayen da ake ciki a wasu sassan duniya daban daban