WASHINGTON DC —
Kwamandojin sojojin Najeriya da na Janhuriyyar Nijar, sun yi wani taro na musamman domin samun hadin gwiwa tsakanin su, don ganin sun kawo karshen 'yan bindigar da suka addabi al'umma a kasashen biyu.
Taron ya biyo bayan yadda 'yan bindigar zamfara kan tsallaka kan iyakar Najeriya, inda suke shiga cikin jihar Maradi yayin da sojojin Najeriya suke fatattakar su daga dazukan jihar Zamfara.
Sai dai yanzu in suka tsallaka Nijar din ma basu tsira ba. Domin karin bayani, saurari rahoton Haruna Dauda Biu..
Facebook Forum