Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Saka Sabon Haraji Akan Kayan Chana


Donald Trump
Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya saka haraji kan karin kayakin China na kimanin dala biliyan $200 da ake shigarwa Amurka, a cigaba da fafatawar da ake yi a fagen cinakayya tsakanin kasashen biyu.

Sabon harajin zai fara aiki ne a makon gobe kuma zai haura da kashi 25% a karshen wannan shekara ta 2018.

A cewar kafar labarai ta Reuters, an tsame agogon lataroni na Apple da Fitbit da kuwa wasu abubuwan kariya daga hadari irinsu hular kwano da kujerun zaunar da yara kanana a mota, daga jerin abuwan da sabon harajin zai shafa.

Wannan mataki da Amurka ta dauka na baya-bayan nan ka iya janyo ramuwar gayya daga China, wadda ta ce za ta yi maraba da duk wata sabuwar tattaunawa da Amurka, to amma ta kuma nuna cewa ba za ta kara shiga tattaunawa da Amurka ba, muddun Amurka ta saka wannan harajin.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG