"A takaice abin da na ke son bayyana a sakona na yau shi ne cewa idan aka dubi yawa da kuma tsananin matsalar, ba tare da dakile akida da kuma manufa ba, ba za mu taba yin galaba kan ta'addnci ba," a cewar Blair a yayin wani jawabi a Cibiyar Huldar Kasa da Kasa da ke Washington, inda ya gabatar da rahoton bincikken cibiyarsa ta rajin kawo sauyi a duniya, Global Change.
"Hakika wasu matakan tsaro sun yi amfani ta wasu fuskoki da dama don haka ya kamata a cigaba da amfani da su. To amma maganar gaskiya ita ce dogaro kan matakan tsaro kadai zai jinkirta tashin hankalin ne kawai," a cewar Blair.
Rahoton mai taken, "Global Extremism Monitor: Violence Extremism in 2017," ya gano cewa duk da daukar matakan dakile tsaurin ra'ayin masu ikirarin kishin Islama ta amfani da karfin soji, matsalar sai ma karuwa ta yi bayan 'yan shekaru. Hakazalika, an samu karuwar kungiyoyin ta'adda a 2017.
Facebook Forum