Sakamakon fusata da suka yi da tashin gwauron zabon da farashin kayayyaki kama daga kwai zuwa makamashi suka yi a ‘yan shekarun baya-bayan nan, masu kada kuri’ar sun yi amfani da damar da suka samu wajen hukunta jam’iyyun masu mulki.
Har yanzu radadin hauhawar farashin na nan bai gushe ba, kuma jam’iyyu masu mulki ake ci gaba da dorawa alhakin hakan yayin zabubbuka.
A Amurka, tsadar kayayyaki ce ta taimaka wa Donald Trump lashe wa’adi na 2 na shekaru 4 a matsayin shugaban kasa bayan yin awon gaba da shi daga fadar White House, kafin daga bisani ya yi ikirarin bogi a kan magudin zabe. Magoya bayansa sun gaza a kokarinsu na sauya rashin nasarar da ya samu ta hanyar yin tururuwa zuwa ginin majalisar dokokin kasar na Capitol a ranar 6 ga watan Janairun 2021.
A bana, an jiyo muryoyinsu ne a akwatunan zabe, inda suka yiwa sabon shugabancin Amurkan da zai jarraba ingancin cibiyoyin dimokiradiya a gida da wajen kasar.
Wannan ra’ayi na kyamar gwamnatocin da ke kan mulki sakamakon hauhawar farashi ya samar da sabbin gwamnatoci a Burtaniya da Botswana da Portugal da Panama da kuma Koriya ta Kudu, inda masu zabe suka dora ‘yan adawa a kan mulki a majalisun dokokinsu. Idan aka nazarci lamarin Shugaba Yoon Suk Yeol. A farkon watan Disamban da muke ciki, shugaban ya kakaba dokar soji a kasar, matakin da nan take majalisar dokokin kasar ta soke. Haka kuma zabubbuka sun girgiza kasashen Faransa da Jamus da Japan da Indiya.
Kasa daya tilo da ba a samu sauyi ba ita ce; Rasha, inda aka sake zabar Vladimir Putin da kaso 88 cikin 100 na kuri’un da aka kada, tarihin da aka kafa a Rasha bayan rushewar tarayyar Soviet.
Moscow ta ci gaba da gudanar da yakin da ta kaddamar a kan Ukraine, inda take samun gagarumar galaba wajen mamaye yankuna. Babbar tambayar a nan ita ce wane irin tasiri dawowar Trump fadar White House za ta yi ga wannan rikici.
Trump sha alwashin kawo karshen yakin cikin kwana guda. mutane da dama a Ukraine da wasu kasashen Turai na fargabar hakan na iya nufin ya goyi bayan Putin tare da dakatar da tsarin da ake kai a yanzu.
A Gabas ta Tsakiya, Isra’ila na ci gaba da yakin da take yi a Gaza inda ta fadada zuwa Lebanon, inda ta ragargaje kungiyar Hizbullahi mai samun goyon bayan kasar Iran. A Syria, gamayyar kungiyoyin ‘yan tawaye sun hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad kuma yanzu su ke neman su mulki kasar.
A bangaren kasuwanci, kamfanoni a fadin duniya na fama da yadda zasu rungumi kirkirarriyar basira. Ana iya jumlancewa masu zuba jari irin mamayar da kamfanonin fasaha suka yi da cewa, kamfanonin fasaha 7, yanzu mashahuran kamfanonin fasaha da ake yiwa lakabi da “Magnificent Seven” ne suka mamaye kaso 1 bisa 3 na jamlanr hannayen jarin da ake juyawa a kasuwar S&P 500 ta Amurka.
Elon Musk, dake jagarantar daya daga cikin kamfanonin, Tesla, mashawarcin kuma mai daukar nauyin zababben Shugaban Trump. Abin da ake jira a gani shine, gamayyar Musk da Trump a fagen mulki zata zayyana yadda shekarar 2025 zata kasance.
-Reuters