Sojojin Isra’ila sun ce wani makamin rokar da aka harba daga Yemen ya abka wani yankin Tel-Aviv da sanyin safiyar yau Asabar inda mutane 16 suka dan ji rauni.
Harin ya biyo bayan wasu jerin hare-haren saman Isra’ila a babban birnin Yemen Sana’a, cibiyar mayakan Houthi, da wata tashar jirgin ruwa a Hodeida wanyayi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 9, kasa da kwanaki 2 da suka gabata mai zaman harin martanin hare haren Mizile da na jirage marasa matuka da mayakan Houthi masu samun goyon bayan Iran suka kai Isra'ila.
Sojojin Isra’il sun ce mayakan Houthi sun harba makaman mizile da jirage marasa matuka sama da 200 a yakin Isra’ila da Hamaz a Gaza.
Sannan, 'yan kungiyar mayakan na Houthi suna ta kai farmaki ta ruwa a bahar maliya da tekun Aden. A Gaza, anyi jana'izar mutane goma sha taran (19) aka kashe a farmakin na Isra'ila.
Dandalin Mu Tattauna