Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rugujewar Gini A Jos: Chidera Denis Na Daga Cikin Wadanda Suka Tsallake Rijiya Da Baya


Gini da ya ruguje
Gini da ya ruguje

Hatsarin da ya faru ranar Juma’a shi ne mafi muni da aka gani tun bayan wanda ya faru a watan Nuwamban 2021, a lokacin da wani katafaren gini ya ruguje a birnin Legas har akalla mutane 45 suka mutu.

Bayan da ta kammala daukar darasi a ajin farko da safe, wata daliba ‘yar Najeriya ‘yar shekara 16 mai suna Chidera Denis, ta zauna jiran ta hadu da takwarorin karatunta don rubuta jarrabawar karshen zango. Malamai sun shirya yin bitar karshe kafin jarabawar.

Bayan wani dan lokaci, Chidera ta makale a karkashin tarkacen gini, yayin da ginin makarantarsu ya ruguje kwatsam, inda dalibai ke zaune.

Chidera na daga cikin wadanda suka taki sa'a a ranar. Rugujewar makarantar Saint Academy da ke karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato ta yi sanadin kashe dalibai 22 a ranar Juma’a, tare da jikkata wasu fiye da sha biyu da ke jinya a asibiti, ciki har da abokiyar Chidera da ta yi tunanin karshenta ya zo.

"Ta ce ta san za ta mutu, idan an cece ni, in gaya wa mahaifiyarta," abin da Chidera ta shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP kenan kwana daya bayan aukuwar bala'in.

"Sai na ce mata ta daina irin wannan maganar, za mu rayu, Allah na tare da mu."

Mahaifiyar Chidera Mrs. Amaka Denis ta kula da ita a asibiti a safiyar Asabar. Ya zuwa lokacin bata ga danta ba, wanda shi ma ya ke zuwa makarantar.

Kakakin Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), Yohanna Audu, ya shaida wa kamfanin dillancin Labarai na AFP a ranar Asabar cewa, an kawo karshen ayyukan ceto, bayan afkuwar bala’in wanda shi ne faduwar gini na baya-baya da aka gani a Najeriya.

Audu ya ce an samu asarar rayuka 22, kuma dukkan su dalibai ne.

"Ina kusa da wani da ya mutu," a cewar Chidinma Emmanuel 'yar shekara 14. "Ya fado kan hannuna har ya karye, tarkacen ginin da suka fada a kansa ne silar mutuwarsa."

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga kasar.

Kwana daya bayan aukuwar lamarin, mutane 58 ke kwance a asibiti yayin da aka salami wasu 74, a cewar kwamishinan yada labarai na jihar Musa Ibrahim Ashoms, a cikin wata sanarwa ranar Asabar.

Rushewar gine-gine dai ya zama ruwan dare a kasar da ta fi yawan al'umma a Afirka.

Hatsarin da ya faru ranar Juma’a shi ne mafi muni tun bayan wanda ya faru a watan Nuwamban 2021, a lokacin da wani katafaren gini da ake kan ginawa a birnin Legas ya ruguje tare da kashe akalla mutane 45, galibinsu ma’aikatan ginin ne.

Rashin ingancin aiki, rashin sa ido, da kuma cin hanci da rashawa yawanci su ake dora laifin a kai.

Ashom ya ce nan take dai ba a san ko me ya janyo rugujewar ginin ba na jihar Filato, amma mazauna yankin sun ce rugujewar ta faru ne bayan da aka shafe kwanaki uku ana ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang "ya jaddada bukatar dukkan masu harkar gine-gine su mika tsarin gininsu ga hukumar kula da gine-gine da ke Jos don duba shi da tantancewa," a cewar Ashoms.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG