Akalla mutane goma ne aka kashe a wasu hare-hare biyu da aka kai ta sama ranar Juma’a a tsakiyar Gaza, ciki har da yara biyu da mata hudu.
Falasdinawa a birnin Rafah da ke kan iyaka sun ba da rahoton kazamin fada a 'yan kwanakin nan, yayin da sojojin Isra'ila ke kara fadada hare-haren da suke kai wa a kudancin kasar, tare da kwace iko da daukacin iyakar Gaza da Masar.
Fadan da ake gwabzawa a Rafah ya sa Falasdinawa sama da miliyan 1 tserewa, wadanda akasarinsu sun riga sun yi gudun hijira a farkon yakin.
A yanzu haka suna neman mafaka a sansanonin wucin gadi da sauran wuraren da yaki ya ruguza, inda ba su da matsuguni, abinci, ruwa da dai sauran abubuwan da ake bukata na rayuwa, in ji Majalisar Dinkin Duniya.
Hare-haren da jiragen yakin Burtaniya da Amurka suka kai kan 'yan tawayen Houthi na Yaman sun kashe akalla mutane 16 tare da jikkata wasu 42, kamar yadda 'yan tawayen suka sanar a yau Juma'a. Wannan shi ne adadi mafi girma da aka amince da shi a bainar jama'a.
'Yan Houthi na kasar Yemen dai sun ce za su cigaba da kai hare-hare kan jiragen ruwa na tekun Bahar Maliya domin nuna goyon bayansu ga Falasdinawa muddin Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare a kansu.
Yakin Isra'ila da Hamas ya kashe Falasdinawa sama da 36,000, a cewar ma'aikatar lafiya, wanda bai banbance tsakanin mayaka da fararen hula ba.
Isra'ila ta kaddamar da yakinta a Gaza ne bayan harin da kungiyar Hamas ta kai a ranar 7 ga Oktoban 2023, inda mayakan suka kutsa kai zuwa kudancin Isra'ila, inda suka kashe mutane kusan 1,200 - akasarinsu fararen hula - tare da yin garkuwa da kusan 250.