Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Duniya Ta Umurci Isra'ila Ta Dakatar Da Kai Farmaki A Rafah


kotun kasa da kasa ICJ
kotun kasa da kasa ICJ

A ranar Juma'a ne babban kotun duniya ICJ ta umarci Isra'ila da ta dakatar da hare-haren da take yi a Rafah , birnin da ke kudancin Gaza inda Falasdinawa sama da miliyan daya suka nemi mafaka a cikin mawuyacin hali.

Ko da yake da wuya Isra’ila ta bi wannan umarni, wanda babbar kotun Majalisar Dinkin Duniya ba ta da hurumin aiwatar da shi, amma hukuncin da aka yanke zai kara matsin lamba kan kasar.

A ci gaba da kalubalantar bacin ran da kasashen duniya suka yi kan rikicin jin kai a yankin, sojojin Isra'ila sun ci gaba da kai munanan hare-haren da suka kaddamar sakamakon hare-haren Hamas na ranar 7 ga watan Oktoba.

Tattaunawar tsagaita bude wuta ta ci tura, duk da matsin lamba da ake yi a gida na firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu na ganin an sako mutanen da a ka yi garkuwa da su a Gaza.

Umurnin na ICJ ya biyo bayan rokon gaggawa da kasar Afirka ta Kudu ta gabatar a wani bangare na shari’ar da take ci gaba da yi a kotun da ke birnin Hague na kasar Netherlands, inda ta zargi Isra’ila da aikata kisan kiyashi a hare-haren da ta shafe watanni ana kai wa Gaza, zargin da Isra’ila da Amurka suka musanta.

Mai yiyuwa ne shari'ar za ta dauki shekaru ana warwarewa, amma Afirka ta Kudu ta nemi umarnin wucin gadi don kare Falasdinawa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG