Harin da aka kai a karshen mako da ya haddasa gobara tare da kashe mutane da dama a wani sansanin gudun hijira da Falasdinawa fararen hula ke matsuguni, ya janyo wani sabon tofin Allah tsine.
Isra'ila, ta ce a ranar Larabar da ta gabata dakarunta sun kwace hanyar Philadelphi mai nisan kilomita 14 a kan iyakar Gaza da Masar, wanda take zargin ana amfani da su wajen safarar makamai.
Kamfanin dillancin labaran Masar daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Qahera News mai alaka da gwamnatin kasar ta ce, "Isra'ila na amfani da wadannan zarge-zargen ne domin tabbatar da ci gaba da kai farmaki kan birnin Rafah da kuma tsawaita yakin da nufin siyasa."
Wani wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa an yi ta artabu da bindigogi a unguwar Zeitun da ke birnin Gaza a arewacin kasar, inda shaidun gani da ido suka ga tarin hayaki yana tashi a kan sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia da kuma Beit Lahia.
Harin da Isra'ila ta kai a karshen mako da kuma gobarar da ta barke a sansanin Falasdinawa da ke Rafah, ta kashe mutane 45 a cewar jami'an Gaza, lamarin da ya sa aka shafe kwanaki biyu ana tattaunawa a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.
Mai baiwa Isra'ila shawara kan harkokin tsaro Tzachi Hanegbi ya ce za a iya ci gaba da yakin har zuwa karshen shekara.
Amurka dai na daga cikin kasashen da ke kira ga Isra'ila da ta kaurace wa hare-haren na Rafah saboda hadarin da ke tattare da fararen hula.
Sai dai fadar White House ta fada jiya cewa kawo yanzu bata ga Isra'ila ta take dokar shugaba Joe Biden ba.
Kame mashigin Rafah da Isra'ila ta yi, ta kara hana kai kayan agaji ga al'ummar Gaza miliyan 2 da dubu 400 tare da rufe babbar hanyar fita daga yankin.
~ AFP
Dandalin Mu Tattauna