Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Soke Umarnin Da Ta Yanke Na Katse Tashar Bidiyon AP Kai Tsaye A Gaza


International correspondent of AP reports live from the network's office in the West Bank. May 5, 2024.
International correspondent of AP reports live from the network's office in the West Bank. May 5, 2024.

Ministan Sadarwa na Isra'ila Shlomo Karhi ya ce ya soke umarnin bayan da ya zargi kamfanin dillancin labarai na AP da saba sabuwar dokar hana bayar da hotunan Gaza zuwa ga tashar Al Jazeera da ke Qatar.

Isra'ila ta ja da baya kan matakin da ta dauka na rufe tashar bidiyo kai tsaye ta kamfanin dillancin labarai na AP dake Gaza a ranar Talata, bayan wata zanga-zangar da kamfanin dillancin labaran Amurka ya yi da kuma nuna damuwa daga fadar White House.

Ministan Sadarwa na Isra'ila Shlomo Karhi ya ce ya soke umarnin bayan da ya zargi kamfanin dillancin labarai na AP da saba sabuwar dokar hana bayar da hotunan Gaza zuwa ga tashar Al Jazeera da ke Qatar.

"Yanzu na ba da umarnin soke aikin da kuma mayar da kayan aikin ga tashar AP," in ji Karhi a wata sanarwa, bayan da Amurka ta yi kira ga Isra'ila da ta sauya matakin.

Umarnin na farko da Karhi ya bayar a ranar Talata ya ce masu binciken ma'aikatar sadarwa sun "kwace kayan" na AP bisa umarnin da gwamnati ta amince da shi "bisa ga doka".

A wata sanarwa da ta fitar bayan wannan odar, kamfanin dillancin labaran AP ya ce ya yi Allah wadai da matakin da gwamnatin Isra'ila ta dauka.

AP ta ce Al Jazeera na daga cikin dubban abokan cinikayya da ke karɓar labaran bidiyo kai tsaye daga ofishin dillancin labaran.

Daraktan yada labaran duniya na AFP Phil Chetwynd ya ce umarnin farko na Isra'ila "hari ne kan 'yancin 'yan jarida".

A wannan watan ne aka yanke tashar Aljazeera mai hedkwata a kasar Qatar daga watsa labarai a Isra'ila bayan da gwamnatin Firai Minista Benjamin Netanyahu ta kada kuri'ar rufe ta saboda labaran da ta ke watsawa kan yakin Gaza.

An rufe ofisoshin gidan talabijin na Aljazeera na Urushalima, an kuma kwace kayan aikin sa, sannan an janye amincewar tawagarsa.

Bayan da aka ba da sanarwar dawo da kayan aikin AP, RSF ta ce a kan shafin X cewa,

"Hani kan @AlJazeera shima dole ne a sauya shi nan take- kuma ya kamata kasashen duniya su nuna irin goyon bayan da suka nuna a yau."

Yakin Gaza ya barke ne bayan harin da Hamas ta kai kan Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 1,170, galibi fararen hula, a cewar wani alkaluman hukumomin Isra'ila.

Hamas ta kuma yi garkuwa da mutane 252, sai dai 124 daga cikinsu sun rage a Gaza ciki har da 37 da sojojin suka ce sun mutu.

Harin ramuwar gayya da Isra'ila ta kai kan Hamas ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 35,647 a Gaza, wadanda kuma akasarinsu fararen hula ne, a cewar ma'aikatar lafiya ta yankin Hamas.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG