"Dole ne a dakatar da wadannan ayyukan. Babu wani wuri da fararen hula Faladinawa su ke zaune cikin kwanicyar hankali a Rafah," in ji Macron a kan shafin X.
"Ina kira da a mutunta dokokin kasa da kasa da kuma tsagaita bude wuta nan take."
Ma'aikatar lafiya a Gaza ta Hamas ta ce adadin wadanda suka mutu ya karu zuwa 45 daga hare-haren da Isra'ila ta kai cikin dare, wanda ya haddasa gobara da ta kashe mutanen da suka rasa matsugunansu a cikin tantunansu, wadanda yawancinsu mata da yara ne.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce tana gudanar da bincike kan rahotannin fararen hula da aka kashe a hare-haren, wanda ya janyo tofin Allah tsine a kasashen Larabawa.
Dandalin Mu Tattauna