Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Isra'ila Ya Halaka ‘Yan Gudun Hijira 35 A Rafah - Likitocin Falasdinawa


Rafah, Zirin Gaza, Mayu 26, 2024
Rafah, Zirin Gaza, Mayu 26, 2024

Ma'aikatan kiwon lafiya na Falasdinawa sun ce harin da Isra'ila ta kai ta sama ya kashe akalla mutum 35 a ranar Lahadin da ta gabata tare da kai hari kan tantunan 'yan gudun hijira a kudancin birnin Rafah.

WASHINGTON, D. C. - Wasu da dama kuma sun makale cikin tarkacen wuta. Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta ce mata da kananan yara su ne mafi yawan wadanda suka mutu da kuma wasu da dama da suka jikkata sakamakon wannan harin.

Rafah
Rafah

Hare-haren dai ya zo ne kwanaki biyu bayan da kotun kasa da kasa ta umurci Isra'ila da ta kawo karshen hare-haren soji a Rafah, inda fiye da rabin al'ummar Gaza miliyan 2.3 suka nemi mafaka kafin kutsawar Isra'ila a farkon wannan wata. Dubun dubatar mutane ne suka rage a yankin yayin da wasu da dama suka tsere.

Hotunan wurin da aka kai hari mafi girma sun nuna barna sosai.

Rafah - Zirin Gaza Mayu 26, 2024.
Rafah - Zirin Gaza Mayu 26, 2024.

Sojojin Isra'ila sun tabbatar da kai harin, kuma sun ce sun kai hari kan cibiyar Hamas ne tare da kashe wasu manyan mayakan Hamas biyu. Ta ce tana gudanar da bincike kan rahotannin da ke cewa an jikkata fararen hula.

Ministan tsaro Yoav Gallant ya kasance a Rafah ranar Lahadi kuma an yi masa bayani kan "zurfafa ayyukan" a can, in ji ofishinsa.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG