A cewar ma’aikatan lafiya, harin Isra’ila ya hallaka akalla mutane 12 a wani gida dake yankin Jabalia dake arewacin Gaza da safiyar yau Laraba, haka kuma akalla mutane 10 sun bata a yayin da ake ci gaba da aikin ceto. Harin motar atilari ya kashe wani mutum guda dake kusa da wurin, a cewarsu.
Hussam Abu Safiya, daraktan asibitin Kamal Adwan dake Beit Lahiya, daya daga cikin asibitocin dake dan aiki a arewacin zirin, yace an sha kaiwa asibitin harin bam ta kowane bangare ba tare da gargadi ba, a daidai lokacin da muke kokarin ceton wani mutum da ya samu rauni a dakin kulawar musamman a jiya Talata.
“Sakamakon kama ma’aikatan jinya da likitoci da kuma hana tawagar da za ta canjesu shiga asibitin, yanzu muna rasa marasa lafiyar da suka samu rauni a kullum wadanda ka iya rayuwa idan da akwai kayayyakin aiki,” kamar yadda ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters a cikin wani gajeran sako.
“An yi rashin sa’a, ba a bari a shigo da abinci da ruwan sha, kuma ba a barin motar daukar marasa lafiya ko guda ta shiga arewacin Gaza.”
Akwai mutane 85 da suka jikkata, ciki harda mata da yara, a asibitin, shida na dakin kulawar musamman. An Kawo yara 17 da alamomin tamowa sakamakon karancin abinci. daya daga cikinsu ya mutu a jiya saboda rashin ruwa, kamar yadda Abu Safiya yace.
-Reuters