Wannan lamarin dai ya sa dubban Falasdinawa tserewa a ranar Litinin din nan daga yankin da aka riga aka lalata a farkon makonnin yakin da aka kwashe watanni tara ana yi.
Kutsen da aka yi a gabashin birnin Gaza ya fadada ayyukan da Isra'ila ke yi a arewacin yankin da Isra'ila ta yi wa kawanya, yankin da Isra'ila ta ce ta kwace iko da shi watannin da suka gabata.
An gwabza kazamin fada a makonnin farko na yakin, sai dai ya mamaye birnin na Gaza da kewaye, kuma sojojin Isra'ila sun hana yawancin mutane komawa gidajensu.
Amma dubban Falasdinawa da dama ne suka rage, suna zaune a rugurjen gidajensu ko matsugunansu.
Yakin ya faro ne a watan Oktoban bara, bayan da mayakan Hamas suka kai hari cikin Isra’ila, wanda ya halaka daruruwan mutane.
Isra’ila a nata martanin ta halaka dubban Falasdinawa a hare –haren martani da take kai wa kan Hamas.
-AP
Dandalin Mu Tattauna