Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Gano Gawarwakin Mutane Da Dama A Gaza


Shugaban Amurka Joe Biden ya ce jami'ansa sun tuntubi Isra'ila wadda ta tabbatar da gano gawarwakin a Gaza. Biden ba shi da tabbacin adadin gawarwakin. Ya kuma kara da cewa ba shi da 'yancin tantance gawarwakin a halin yanzu.

Isra'ila ta ce ta gano gawarwakin mutane da dama a Gaza a lokacin da ake gwabza fada, kuma sojojinta na kokarin zakulo gawarwakin domin tantance ko su wanene, wanda zai dauki tsawon sa'o'i da dama.

To sai dai Isra’ilar ta bukaci jama'a da su guji yada jita-jita game da gawarwakin.

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce ma'aikatansa sun tuntubi Isra'ila wadda ta tabbatar da gano gawarwakin a Gaza. Biden ba shi da tabbacin adadin gawarwakin. Ya kuma kara da cewa ba shi da 'yancin tantance gawarwakin a halin yanzu.

Akalla Falasdinawa 40,691 ne aka kashe yayin da wasu 94,060 suka jikkata a hare-haren da sojojin Isra'ila suka kai a zirin Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, a cewar ma'aikatar lafiya ta yankin a wata sanarwa a jiya Asabar.

Yakin ya soma ne lokacin da kungiyar ta'addanci ta Hamas ta kai hari kan Isra'ila, inda ta kashe mutane 1,200 tare da yin garkuwa da kusan Isra'ilawa 250, kamar yadda kididdigar Isra'ila ta nuna.

A ranar Assabar an gwabza fada tsakanin sojojin Isra'ila da mayakan Falasdinawa a yankin yammacin gabar kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye, a daidai lokacin da Isra'ila ke ci gaba da kai farmakin soji a birnin Jenin.

Daruruwan sojojin Isra'ila na ciga da kai samame tun ranar Laraba, a daya daga cikin hari mafi girma da suka kai a gabar yammacin kogin Jordan cikin watanni.

Da ya ke zantawa da manema labarai a bakin Tekun Rehoboth a jihar Delaware, Biden, ya ce "har yanzu yana da kwarin gwiwa," game da yarjejeniyar tsagaita bude wuta don dakatar da rikicin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG