Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Hari, Cikin Dare, Ya Kashe Mutane 9 A Kudancin Gaza


Khan Younis, Gaza
Khan Younis, Gaza

Wani hari da Isra'ila ta kai ya kashe akalla mutane tara a birnin Khan Younis da ke kudancin Gaza, a cewar jami'an kiwon lafiya na Falasdinu a ranar Talata.

An kai harin ne kwana daya bayan da Isra'ila ta ba da umarnin mutane su fice daga wasu sassan birnin, gabanin wani samame.

Falasdinawa a Khan Younis
Falasdinawa a Khan Younis

Harin na cikin dare ya afka ne da wani gida da ke kusa da asibitin European Hospital, wanda ke cikin yankin da Isra'ila ta ce a kwashe mutane daga cikinta.

Bayan da aka ba da umarnin ficewa na farko, rundunar sojin ta ce ba a hada da wurin ba, amma daraktan ta ya ce an riga an kwashe yawancin marasa lafiya da likitocin daga asibitin.

Wani mtutm dauke da yaran sa a Khan Younis
Wani mtutm dauke da yaran sa a Khan Younis

Sam Rose, darektan tsare-tsare a hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ‘yan gudun hijirar Falasdinu, wanda aka fi sani da UNRWA, ya fada yau Talata cewa hukumar ta yi imanin cewa kimanin mutane 250,000 na cikin yankin da ake gudun hijira, sama da kashi 10% na al’ummar Gaza mai mutane miliyan 2.3, ciki har da dama da suka tsere daga fada na baya.

Ya ce wasu mutane 50,000 da ke zaune a wajen yankin za su iya zabar barin inda suke saboda kasancewar su kusa da wurin fadan.

An gaya wa mutanen da aka kwashe su nemi mafaka a wani sansani dake baje a bakin teku wanda tuni ya cika da dimbin jama’a da karancin kayan amfani na yau da kullum

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG