Gwamnatin Neja Ta Kori Ma’aikata Sama Da 300

Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello (Hoto: Twitter, Gwamnatin jihar Neja)

Gwamnatin jihar Nejan Najeriya ta sanar da korar ma'aikatanta guda 328 daga bakin aiki saboda samunsu da laifuffuka daban-daban da suka karya dokokin aikin gwamnati a jihar.

A wani taron manema labarai shugaban hukumar kula da harkokin ma'aikata na jihar Alhaji Shehu Yusuf Galadima, ya ce ko baya ga wadanda aka korar akwai wasu guda 380 da aka sa suka yi ritaya.

"An dauki ma'aikata, kuma wasunsu ma malamai ne, kuma wai su za su koya 'ya'yanmu, ko likita ne in ya zama na bogi, za a rasa rayuka." In ji Galadima.

Kungiyar kwadagon jihar Nejan ta ce tana da masaniya akan wasu ma'aikatan da aka kora amma kuma ba ta da labarin korar wasun kamar yadda shugaban kungiyar kwadagon jihar Kwamared Yakubu Garba ya ce.

"Abin da nake so na yi ba'asi akai shi ne, duk ma'aikacin da aka ce an kore shi akan an kama shi da takardar bogi, to ka ga ita kungiyar kwadago, kungiya ce mai bin doka da oda, ba ma wani ainihin dama da za mu ce za mu kare mutumin da aka tabbatar laifinsa ya tabbata." in ji Kwamared Garba.

Ko da yake, wannan yana zuwa ne a daidai lokacin da daruruwan matasa suka kammala karatu a matakai daban-daban amma babu aikin yi a jihar.

Sai dai Gwamnatin jihar Nejan ta ce ta dauki sabbin ma'aikata guda 1,133 domin maye gurbi da kuma samar da aikin yi ga wasu matasan.

Saurari rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari:

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Neja Ta Kori Ma’aikata Sama Da 300