Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Zanga-Zanga Sun Rufe Titin Abuja Zuwa Kaduna Kan Matsalar Satar Mutane A Kasar


Masu Zanga-Zanga Sun Toshe Titin Kaduna Zuwa Abuja
Masu Zanga-Zanga Sun Toshe Titin Kaduna Zuwa Abuja

Mazauna garin Gauraka da ke karamar hukumar Tafa a jihar Naija sun rufe titin Abuja zuwa Kaduna, a wata zanga-zanga, inda suke neman gwamnati ta kawo karshen matsalolin masu garkuwa da mutane da ayukan ‘yan bindiga a jihar da ma kasa baki daya.

Masu zanga-zangar sun kona tayoyi tare da tsayar da zirga-zirgar ababen hawa a kan babban titin na Abuja zuwa Kaduna da safiyar yau fitinin inda suka bukaci gwamnatocin jihohi da ma na tarayya su karfafa matakan tsaro tare da kawo karshen yawan hare-haren yan bindiga a yankin.

Wannan zanga-zangar na zuwa ne bayan afkawa yankin da ‘yan bidnidga suka yi a ranakun Asabar da Lahadi inda suka yi awon gaba da akalla mutane 15 tare da hallaka wasu mutane 3.

Masu Zanga-Zanga Sun Toshe Titin Kaduna Zuwa Abuja
Masu Zanga-Zanga Sun Toshe Titin Kaduna Zuwa Abuja

Rahotanni daga garin sun bayyana jita-jitar kutsen mayakan Boko Haram cikin garin na Gauraka biyo bayan sanarwar gwaman Abubakar Bello na Jihar ya bayyana cewa, mayakan na Boko Haram sun kafa tutarsu a wasu yankunan jihar na Neja a witan Afrilu.

Garin Gauraka dai na da nisan kilomita 5 daga fadar gwamnatin Najeria wato babban birnin tarayya Abuja.

Mazaunan yankin sun kuma koka kan cewa, sun dade suna rasa barci sakamakon ayyukan masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa wadanda suka cigaba da addabar mutanen yankin inda suka bayyana cewa, daga watan Janairu zuwa yanzu yan bindiga sun yi awun gaba da mutane sama da 30 daga yankin.

A baya-bayan nan dai, jihar Neja ta fuskanci yawan munanan hare- haren ‘yan bindiga wanda ya yi sanadiyan rasa rayukan mutane sama da 100 da suka hada da jamt’an tsaro ma tare da raba sama da mutane dubu 50 da muhallan su da ke neman mafaka a sansanonin ‘yan gudun hijira na wucin gadi da gwamnatin jihar ta samar.

Tuni dai gwamnan jihar ya nemi taimako daga dukkan masu ruwa da tsaki.

XS
SM
MD
LG