A wani taron shugabanninta da ta gudanar da yammacin ranar Talata, kungiyar kwadagon Najeriya ta yi matsayar sake tsunduma yajin aiki, wannan lokacin na kasa baki daya, domin abin da ta kira kasawar gwamnatin jihar ta Kaduna, na mutunta yarjejeniyar da aka cimma akan lamarin.
Shugaban kungiyar kwadagon Kwamared Ayuba Wabba ya ce sun yi iya bakin kokarinsu na ganin gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya aiwatar da jarjejeniyar da aka cimma a zaman sulhun da gwamnatin tarayya ta jagoranta, amma lamarin ya ci tura.
Ya kara da cewa kungiyar ta kuma aike da wasiku zuwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da Ministan kwadago Chris Ngige, inda ta fadakar da su akan kin mutunta yarjejeniyar da gwamnatin jihar Kaduna ta yi.
Wabba ya ce kungiyar ta yanke shawarar sake komawa yajin aikin ne bayan duk wasu hanyiyo da ta bi na ganin an daidaita lamari sun tashi a tutar babu.
Akan haka ya ce kungiyar ta sanar da dukan hukumomin gwamnati, haka kuma ta umarci dukan kungiyoyin ma’aikata da ke karkashinta da su soma kimtsa ma’aikata domin soma yajin aikin.
Shugaban kwadagon ya zargi gwamnatin ta jihar kaduna da take tanade-tanaden doka, inda ya ce “gwamna Nasir El-Rufai yana mulki irin na soja ne ba mulkin dimokaradiyya ba.”
A ranar 17 ga watan Mayu ne kungiyar kwadagon ta shiga yajin aikin gargadi na kwanaki 5, akan korar dubban ma’aikata a jihar ta Kaduna.
To sai dai ta janye yajin aikin bayan kwanaki 3, biyo bayan sa bakin gwamnatin tarayya, wacce ta jagoranci zaman sasantawa har aka rattaba hannu akan yarjejeniyar sulhu tsakanin kungiyar kwadagon da gwamnatin jihar Kaduna.