Gwamnatin Neja ta ja Kunnuwan Malamai Akan Kalamun Batanci

Mai Martaba Muhammed Sa'ad Abubakar III Sarkin Musulmi.

Gabanin tsayawar watan Ramadan gwamnatin jihar Neja ta ja kunnuwan malamai da su kiyaye kalamunsu su kauce yi kalamun batanci da ka iya harzuka jama'a lokacin azumi.

A yayin da watan Ramadan ke karatowa gwamnatin jihar Neja tace zata kama duk wani malamin da aka samu yana furta kalamai na harzuka jama'a a cikin wa'azinsa.

Gwamnatin jihar dai tace ta dauki matakin ne bisa ga la'akari da yadda kasar Najeriya ke fama da matsalar tsaro musamman a yankin arewacin kasar.

Alhaji Shehu Haruna kwamishana mai kula da harkokin addinai a jihar ya kira malamai ya kuma fada masu gaskiya. Duk wanda ya zo yin wa'azi kada yayi anfani da kalmomin da zasu harzuka mutane saboda ganin halin da kasar ke ciki. Yace ya kira shugaban IZALA dake Jos yayi magana da shi. Yace basu son malami ya zo jihar yana babatu lokacin wa'azi domin a jinjina masa.

A shirin ladabtar da duk malamin da yayi kunnen kashi gwamnatin jihar ta aika da wasika zuwa jami'an tsaro na SSS da sauransu cewa su yi shirin ko ta kwana. Duk wanda ya harzuka mutane da kalamunsa a cafkeshi a kuma hukuntashi. Kasar na bukatar zaman lafiya. Idan babu zaman lafiya babu addini.

Malaman sun ce su shirya shiga watan na Ramadan tare da yin taron tattaunawa tsakaninsu. Imam Umar Faruk sakataren majalisar limaman Juma'a a jihar Neja yace sun zauna sun tattauna sun kuma ja hankalin kowa akan cewa watan Ramadan wata ne na hadin kai. Sun ja hankalin mutane akan abubuwan dake kawo rarrabuwa. Sun gargadi kansu su gujewa rarrabuwa wajen ranar daukar azumi. Sun yi istifaki su jira sanarwa daga mai alfarma Sarkin Musulmi akan ranar da za'a fara azumin.

Ranar Juma'a ake jiran ganin watan na Ramadan.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Neja Ta Ja Kunnuwan Malamai Akan Kalamun Batanci -2' 30"