Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Karrama Mata a Abuja da Kayayakin Sana'a


Mata na jiran taimako.
Mata na jiran taimako.

Gidauniyar agaji mai suna "Rock of Ages Empowerment" ta karrama mata dubu daya domin tunawa da ranar matan da suka rasa mazajensu ta sanadiyar rasuwa.

Gidauniyar agaji mai suna "Rock of Ages Empowerment" ta karrama mata dubu daya domin tunawa da ranar matan da suka rasa mazajensu ta sanadiyar rasuwa.

Matan sun yi nasaran samu kayayakin sana’a kamar injin na nika da na dinki da kuma buhunan shinkafa da kuma tsabar kudi dubu ashiri-ashiri.

Shugaban wannan Gidauniya Evangelist Ignatius Eziego, yace tashi sa a Maiduguri da kuma ganin yanda matan da suka rasa mazajensu ke wahala ne yasa ya dauki wannan matakin.

Wata daga cikin wadanda suka amfana a bara Hussaina Ibrahim, tace yanzu tana mai dogaro da kanta kuma yayi alkawarin daukar nauyin karatu danta.

Evangelist Eziego, ya bada kekunan dinki dari da arbain da shida, mata dari da talatin da shida an basu kudi dubu ashiri- ashiri sauran mata dari bakwai da goma sha takwas an basu buhunan shinkafa da zasu fara sanar abinci dashi.

Shakara na hudu kennan da gidauniyar ta fara bada irin wannan tallafi mata sun zo ne daga jihohi shida wadanda suka hada da Borno, Lagos, Plateau, Kwara, Kogi da birnin taraiya Abuja,a halin yanzu an kashe kudi sama da Naira miliyan hamsin a cikin shekaru hudu.
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:37 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG