A cigaba da tunawa da cikar Najeriya shekaru dari da kafuwa, wato lokacin da turawan milkin mallaka suka hade kudanci da arewacin kasar, an bude gasar iya girki a Abuja.
Hukumar Yawon Bude Ido Da Haba-haba Da Jama'a ta shirya gasar iya girkin a Abuja inda gidajen abinci, masaukan baki da kamfanonin cimaka ke halarta. Gasar na cikin taron murnar cikan Najeriya shekaru dari da hade kudu da arewa.
Ministan yawon bude ido Edwin Duke da shugaban hukumar Kanayo O. Kanayo sun karfafa cewa Najeriya ta kai wadannan shekarun ne a hade domin albarkacin wadatar abinci da santinsa wanda baya banbanta addini ko kabilar mai cin abincin.
Jami'an siyasa sun yi anfani da gasar da nuna cewa shugaba Jonathan ya dage domin raya harakar noma da kiwo. Babban daraktan hukumar Dr. Munzali Dantata ya zanta da Muryar Amurka. Musamman ya abanci runfar kamfanin Dangote da yace ta birgeshi haka ma Otel din Transcorp.
Bayan girka tuwo da miyar kuka da taushe, egusi da amala shi kuma kamfanin Dala daga Kano ya zo da kunun tsamiya. Shugaban kamfanin Ali Safiyanu Madugu yace yadda ake hada kunnun tsamiya a gargajiyance haka suke hada duk kayan da ijina kafin su zubashi cikin mazubi yadda ba zai baci ba har na tsawon shekara guda.
Ga karin bayani daga Nasiru Adamu El-Hikaya.
Hukumar yawon bude ido da haba-haba- da jama'a ta Najeriya ta shirya gasar iya girki a Abuja a cigaba da bikin hadewar kudanci da arewacin kasar zama kasa daya shekaru dari da suka gabata.
WASHINGTON, DC —