Gwamnatin Najeriya Ta Fara Sa Ido Kan Sabon Nau'in Omicron Na Korona

NCDC COVID-19 PIC

Hukumar kula da cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta ce tana sa ido kan bayanan da ke fitowa kan sabon nau'in cutar COVID-19 na Omicron, wanda aka fara ganowa kwanan nan a kasar Afirka ta kudu.

Masana kiwon lafiya na ganin cewa sabon nau’in cutar ta korona birus na saurin yaduwa kuma tuni ta gano wannan nau’i ya haifar da sabbin matakan hana tafiye-tafiye da aka yi niyya a kasashen kudancin Afirka.

A cikin wata sanarwa da babban daraktan hukumar NCDC, Dokta Ifedayo Adetifa ya sanya wa hannu, hukumar ta ce, babu wata shaida a game da shakku da ake yi a kan karfin wannan sabon nau’in, da cewa zai fi karfin matakan kariya ko kuma maganin rigakafin a halin yanzu.

A yayin da hukumar lafiya ta duniya wato WHO da masu bincike a duk faɗin duniya suke kan aikin gaggawa don samun fahimtar yiwuwar tasirin wannan sabon nau’in na COVID-19 da kuma karfinsa a kan alluran rigakafi da ma hanyoyin warkewa, hukumar NCDC ta bukaci 'yan Najeriya da su dauki matakan karıya da suka dace.

Hukumar NCDC dai ta shawarci ‘yan Najeriya da su yi amfani da damar da ake da su a halin yanzu don yin allurar rigakafin cutar COVID-19 don kare kan su.

Kazalika, hukumar NCDC ta sake nanata bukatar 'yan kasa su bi matakan karıya da ma’aikatan kiwon lafiyar jama'a suka shimfida kaman bada tazara tsakanin juna, sanya takunkumin fuska, wanke hannu a kai-a-kai da dai sauransu.

"Kamata yayi duk ‘yan kasa su kaucewa yin tafiya zuwa kasashen da ake samun karin masu dauke da sabon nau’in COVID-19 wato Omicron da kasashen da aka sami rahoton bullar cutar ta Omicron," in ji NCDC.

NCDC ta ce kamata ya yi yan kasa su guji duk tafiye-tafiye da bai zama dole ba na cikin gida da waje, ta na mai cewa idan ya zama dole mutum ya yi tafiya sai a yi taka-tsan-tsan da matakan karıya da ka'idojin balaguron da kwamitin gwamnatin tarayya mai kula da harkokin lafiya ta PSC-COVID-19 ta kafa don hana hadarin shigo da kwayar cutar ko nau'ikanta zuwa Najeriya.

Haka kuma NCDC ta yi kira ga masu kasuwanci, shugabannin addini, da ma’aikatan gwamnati da su dauki nauyin wayar da kan al’umma ta hanyar tabbatar da cewa mutane a cikin wurarensu sun sanya takunkumin rufe fuska tare da bada tazara tsakanin juna don yaki da cutar.