Kwamitin PSC dai ya bukaci a rage cunkoso a masallatai, haka kuma a yi amfani da filayen sallar Idi da ke sarari a maimakon masallatai da ke rufe, saboda samun isasshen iska.
A cikin wata sanarwa da ke dauke da sa hannun sakataren gwamnatin Najeriya kuma shugaban kwamitin shugaban kasa kan yaki da cutar Covid-19, Boss Mustapha, ta ce jihohin da gwamnati ta yi gargadi na a kula sosai sun hada da Legas, Oyo, Ribas, Kaduna, Kano, Filato da babban birnin tarayya Abuja.
Sanarwar ta kara da cewa an kuma yi wa sauran jihohi gargadin kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana da kuma ci gaba da aiwatar da dokar kare kai.
Hukumar kula da cututtuka masu saurin yaduwa a Najeriya wato NCDC, ta bayyana cewa, an sami sabbin masu dauke da cutar korona birus 203 a ranar lahadi kawai a fadin kasar inda mutum daya ya rasa ransa.
Alkaluma daga shafin yanar gizon hukumar ta NCDC sun yi nuni da cewa, jihar Legas ke kan gaba da adadi na 186 a cikin mutane 203 da suka kamu da cutar wanda shi ne adadı mafi yawa, sai jihar Edo da mutane 4, Oyo mutane 4, Ribas mutane 4, sai babban birni tarayya da mutane 3 da kuma Kwara da ta sami mutane 2.
Babban manajan kula da yaduwar cutar korona birus na kasa karkashin hukumar NCDC, Dakta Mukhtar Muhammad ya tabbatar da batun sa ido kan jihohin 6.
A halin yanzu adadin wadanda suka kamu da cutar a Najeriya sun kai 169,532 inda mutane 164,699 suka warke, mutane 2,127 kuma suka rasa rayukansu.
Karin adadin wadanda suka kamu da cutar na zuwa ne bayan da gwamnatin Najeriya ta ayyana cewa za ta sa ido kan jihohi 6 sakamakon yiyuwar sake bullar cutar a karo na 3 saboda nau’in cutar ta Delta da aka gano a kasar wanda ake ganin ya fi saurin yaduwa.
A fadin duniya dai, cutar korona birus ta halaka kimanin mutane miliyan 4 da dubu 86 da 242 tun bayan bullarta ta farko a birnin Wuhan na kasar China a watan disamban shekarar 2019 kamar yadda alkaluman kididdiga daga kamfanin dillancin labarai na AFP suka ruwaito.