Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Na Shirin Daukar Mataki Kan Wadanda Suka Ki Karbar Rigakafn Korona.


ALLURAR RIGAKAFI
ALLURAR RIGAKAFI

Gwamnatin Najeriya ta ce tana duba yiwuwar daukar matakan hukunta ‘yan kasar da suka ki amincewa su karbi allurar rigakafin cutar korona.

Babban daraktan hukumar kiwon lafiya matakin farko ta kasa (NPHCDA) Faisal Shu’aib ne ya bayyana haka, a wani taron manema labarai da aka gudanar a ofishin hukumar na Abuja.

Daraktan yace gwamnati za ta iya amfani da tsarin doka kan mutanen saboda kin amincewa da yin rigakafin, wanda hakan zai iya jefa wasu mutane cikin hatsari.

Ya kara da cewa idan mutanen na da ‘yancin kin yin allurar rigakafi, to amma kuma basu da ‘yancin cutarwa ko kuma barazana ga lafiyar wadansu.

Har yanzu dai tsarin karbar allurar rigakafin cutar korona, babu mata masu juna biyu da kananan yara.

Idan za’a iya tunawa a makon da ya gabata ne gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya umurci ‘yan jihar da su yi allurar rigakafin, yana mai cewa daga ranar 15 ga watan Satumba, duk wanda bai yi rigakafin ba za’a haramta masa shiga wuraren taruwar jama’a kamar bankuna da wuraren Ibada.

To sai dai kuma wata kotu a jihar ta ba da umarnin dagatar da daukar wannan matakin na wani lokaci, biyo bayan kara da aka shigar a gabanta kan lamarin.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG