Gwamnatin Mulkin Sojin Nijar Ta Kori Wasu Dakarun Tarayyar Turai Daga Kasar

EUCAPS SAHEL NIGER

Hukumomin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar sun kori wasu sojojin rundunar zaman lafiya ta kungiyar Tarayyar Turai a Sahel wato EUCAP-Sahel da ma shugabar kungiyar daga kasar

AGADAZ, NIGER - Wannan matakin da gwamnatin sojoji ta Nijar ta dauka na zuwa ne lokacin da ya rage watanni hudu wa'adin da hukumomin suka bai wa rundunar ta Eucap Sahel na ficewa daga cikin kasar.

A cikin wasika ce da ministan cikin gida na kasar Nijar ya sanyawa hannu wacce ya aikewa shugaban rundunar Eucap Sahel reshen kasar Nijar ya sanar da baiwa wasu sojojin rundunar su 15 sa'o'i 72 domin ficewa daga cikin kasar ta Nijar bisa zargin su da shigowa cikin kasar ba bisa ka’ida ba kuma sun shigo ba tare da sun sanar da mahukunta ba.

Tun a watan Disamban shekarar da ta gabata hukumomin mulkin sojin a Nijar suka soke yarjejeniyar tsaro da kungiyar tarayyar Turai inda suka bata wa’adin watanni shida domin dakarun tarayyar Turai su fice daga cikin kasar Nijar baki daya.

Malan Moussa Bilal na ‘yan kungiyar farar hula na daga cikin wadanda ke goyan bayan hukumomin, ya kuma yaba da matakin saidai ya ce akwai bukatar bin lamarin a hankali.

A makon da ya gabata hukumomin mulkin sojin kasar ta Nijar suka kori Babban Wakilin Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya a Nijar wanda aka tare shi a filin jirgin sama na birnin Yamai lokacin dawowarsa daga tafiya inda suka bashi umarnin ficewa daga kasar nan take.

To saidai Abdourahmane Bianou wani ‘dan fafutuka a Nijar ya ce akwai bukatar gwamnati ta musu bayani kan wadannan matakai, amma kuma ba dukka ‘yan Nijar ne suka yaba da wannan matakin ba na korar rundunar ta Eucap Sahel yayinda aka samu rarrabuwar kawuna a tsakanin ‘yan kasar ta Nijar.

Kungiyar Tarayyar Turai ta nuna rashin jin dadinta a game da wannan mataki na gwamnatin Nijar na korar sojojin rundunar duk da kuma cewa wa’adin kammala ficewar rundunar bai cika ba.

Saurari cikakken rahoto daga Hamid Mahmud:

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Mulkin Sojin Nijar Ta Kori Wasu Dakarun Tarayyar Turai Daga Kasar  .mp3