Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Mulkin Sojan Nijar Sun Dakatar Da Ayyukan Gamayyar Kungiyoyin ‘Yan Jarida


Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar
Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar

Hukumomin sun kuma ayyana hakan ba tare da bayyana dalilan daukan wannan mataki ba.

NIAMEY, NIGER - Wannan lamari ne da wasu kungiyoyin kare hakkin ma’aikatan watsa labarai ke dauka a matsayin wata babbar barazana ga ‘yancin fadin albarkacin baki duk kuwa da cewa a sanarwar da suka bayar a washe garin juyin mulki 26 ga watan Yuli 2023 sojojin CNSP sun sha alwashin mutunta yarjejeniyoyin kasa da kasa da Nijar ta rattaba wa hannu.

Ministan Cikin Gida, Janar Mohamed Toumba, ne ya sanar da dakatar da ayyukan Gamayyar ta Kungiyoyin ‘Yan Jarida Maison de la Presse ta hanyar wata takardar da ya saka wa hannu ba tare da fayyace makasudin daukan wannan matakin ba, koda yake Sakataren Kungiyar Ma’aikatan Watsa Labarai ta SYNATIC Moudi Moussa na cewa abin ya yi daidai.

To sai dai wani kusa da kungiyar ‘yan jarida ta ONIMED Ibrahim Amadou ya kalubalanci wannan mataki a bisa la’akari da yadda abin ke kama da katsalandan a harkokin cikin gidan kungiyar da ba ta da alaka da harkokin siyasa.

Ministan ya damka al’amuran gudanar da ayyukan kungiyar a hannun wani kwamitin wucin gadi da ya kunshi sakatarensa da na Ofishin Ministan Sadarwa da wasu darektoci, abin da Editan jaridar Le Temps Zabeirou Souley ya ayyana a matsayin wata barazana ga ‘yancin aikin jarida.

Dama tun a watan Disamban da ya gabata ministan cikin gida ya umurci shugabannin gamayyar kungiyoyin ta Maison de La Presse da su jingine zaben da ya kamata a gudanar domin sabunta mambobinta saboda, a cewarsa, abu ne da ka iya zama sanadin tada zaune tsaye.

Wannan dambarwa na wakana a wani lokacin da ma’aikatan kafafen labarai masu zaman kansu ke cikin halin kangin rayuwa sakamakon rashin biyansu albashin watanni da dama, lamarin da ke nasaba da halin fatarar da irin wadanan kafafe suka tsinci kansu wanda kuma ake dangantawa da jerin takunkumin da kasar Nijar ke fama da su sanadiyar juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2026.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Hukumomin Mulkin Sojan Nijar Sun Dakatar Da Ayyukan Gamayyar Kungiyoyin ‘Yan Jarida .MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG