NIAMEY, NIGER - Masana dai sun ce akwai wasu ka’idoji dake kunshe a cikin wannan dambarwa da ta biyo bayan juyin mulkin da aka fuskanta a kasashen uku da ke yankin Afrika ta Yamma.
A tattaunawarsa da Muryar Amurka wani lauya da ke aiki a cibiyar nazari da bincike kan dokokin kasa da kasa, Barista Bachir Amadou, mazaunin Montpellier na kasar Faransa, ya bayyana cewa dokokin ECOWAS sun gindaya wasu sharuda da ya zama wajibi kasa ta cika kafin ta fice daga kungiyar.
Hakazalika, Maitre Bachir ya ce abin da wadanan kasashe suka fada tamkar sanarwa ce suka bayar kan shirin su na ficewa daga CEDEAO domin a ka’idar kungiyar, kasa ba ta ficewa kai tsaye, tilas ne a rubuta wa hukumar gudanarwarta don sanar da ita kuma za a jira tsawon shekara guda kafin kudirin ficewar ya tabbata.
Wannan, in ji shi, na iya zama wata damar samar da sulhu ta yadda kasashen za su canza ra’ayi kuma dalili kenan na kayyade tsawon shekara guda.
Lauyan ya kara da cewa lalle ne kungiyar ECOWAS na da hurumin hukunta dukkan wata kasar da aka yi juyin mulki, amma kuma a gaskiya kungiyar ta yi kuskure game da batun Nijar domin babu inda dokokin kungiyar suka bada damar a yi amfani da karfin soja kan sojojin da suka yi juyin mulki.
Idan wadanan kasashe na son ficewa daga CEDEAO, to lallai sai sun bi hanyar da aka shimfida.
Dokokin kungiyar ta ba su yanci amma su bi ka’ida watakila kafin nan da cikar wa’adin shekara guda a na iya samun maslahar wannan dambarwa.
Saurari cikakken hirarasu da wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna