NIAMEY, NIGER - Bangarorin biyu sun tsayar cewa Nijar za ta biya wadanan kudade a tsawon watanni 12 ta hanyar danyen man da kasar ke sa ran fara sayar wa a kasuwannin duniya daga watan Mayu mai zuwa, tare da sharadin biyan kashi bakwai na kudaden ruwa.
‘Yan fafutika na fatan ganin za a kasafta wadanan kudade a hanyoyi da talakawa za su gani a kasa.
A karshen zaman yarjejeniyar da aka saka wa hannu Firaministan gwamnatin rikon kwarya Ali Lamine Zeine da shugaban CNPC China Zhou Zuokun sun sanar cewa kamfanin ya amince ya bai wa Nijar bashin million 400 na dolar Amurka wadanda kasar za ta biya da danyen man fetur a tsawon shekara guda.
Firaminstan ya yaba da yanayin da bangarorin biyu suka tattauna kan wannan mu'amula saboda yadda aka yi abin cikin tsari irin na ga nawa ga naka injishi, ya kara da cewa zasu yi amfani da wadanan kudaden bashin a fannin tsaron kasa bunkasa ayyukan noma da kiwon lafiya sannan zasu biya wasu daga cikin basusukan ciki da wajen kasa.
Gwamnatin Nijar dai da ta ciyo wannan bashi a wani lokacin da take matukar bukatar kudade domin tafiyar da lamuran mulki ta dauki alkawalin biyan kashi 7 daga cikin 100 na yawansu a matsayin kudin ruwa, amma wani tsohon dan majalissa Hon. Abdoul Moumouni Ghousman na gargadin mahukunta akan yadda za a kasafta wadanan kudade.
A watan mayun da ke tafe ne Nijar ke sa ran fara sayar da danyen manta a kasuwannin duniya ta hanyar bututun da aka gina tsakanin shekarar 2019 zuwa 2022, wanda ke ratsa kasar na tsawon kilomita kusan 2000 tun daga rijiyoyin Agadem dake arewacin jihar Diffa, ratsawa ta jihohin Zinder da Maradi da Tahoua da kuma Dosso kafin ya dangana da tashar jirgin ruwan Seme a jamhuriyar Benin.
An dai bayyana cewa daga cikin ganguna 110,000 da aka fara hakowa a kowace rana ganguna 90000 ne za su shiga kasuwannin duniya inda CNPC China ke da kashi 76 daga cikin 100 yayin da Nijar ke da kashi 24.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5