Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Yi Na'am Da Bukatar Kwashe Sojojinta Daga Nijar


Ganawar jakadiyar Amurka a Nijar da Ministan ciki gida
Ganawar jakadiyar Amurka a Nijar da Ministan ciki gida

Sama da mako guda bayan da hukumomin jamhuriyar Nijar suka bada sanarwar yanke huldar ayyukan soja da Amurka gwamnatin Amurkar ta ce ta yi na’am da wannan mataki saboda haka nan gaba kadan kasashen biyu zasu tattauna kan hanyoyi mafi amfani wajen kwashe sojojin Amurkan daga kasar.

NIAMEY, NIGER - Wannan na zuwa ne washe garin wata hirar da shugaban majalissar CNSP Janar Abdourahamane Tiani ya ce ya yi ta waya da Vladimir Putin game da huldar Russia da Nijar.

Jakadiyar Amurka ta Nijar da Ministan cikin gida na Nijar
Jakadiyar Amurka ta Nijar da Ministan cikin gida na Nijar

A yayin ganawar da aka yi a tsakanin Ministan Cikin Gida, Janar Toumba Mohamed da jakadiyar Amurka a Nijar, Kathleen Fitzgubbon, a wannan Laraba 27 ga watan Maris ne jami’an kasashen biyu suka tattauna kan sanarwar da hukumomin mulkin sojan Nijar suka bayar a ranar 16 ga wata wacce a ciki suka bayyana yanke shawarar tsinke huldar ayyukan soja da kasar Amurka saboda abinda suka kira rashin gamsuwa da halaccin yarjejeniyar da kasashen biyu suka cimma a shekarar 2012 a wani bangare na karfafa matakan yaki da ta’addanci.

A bayyane take sanarwar gwamnatin rikon kwaryar ta Nijar tamkar umurni ne akan bukatar Amurka ta kwashe dakarun 1100 da ta girke a arewacin kasar.

Jakadiyar Amurka a Nijar lokacin da suka tattauna akan batun kwashe sojojin Amurka daga kasar
Jakadiyar Amurka a Nijar lokacin da suka tattauna akan batun kwashe sojojin Amurka daga kasar

Abin da ya sa jakadiya Kathleen Fitzgubbon a ganawarta da ministan cikin gidan Nijar Janar Toumba ta sanar da shi cewa Amurka ta yi na’am da matakin da Nijar ta dauka saboda haka kasar za ta gabatar da wani daftarin da bangarorin biyu za su tattauna kansa domin tsara jadawalin kwashe sojojin na Amurka daga kasa kamar yadda aka wallafa a shafin yanar gizo na ma’aikatar cikin gidan jamhuriyar Nijar.

Jakadiyar Amurka ta jaddada cewa kasarta za ta ci gaba da tallafawa al’ummar wannan kasa kamar yadda aka saba ta hanyar ayyukan raya karkara a karkasin inuwar hukumar USAID.

Jakadiyar Amurka a Nijar Kathleen Fitzgubbon da Ministan cikin gida na Nijar Toumba Mohamed
Jakadiyar Amurka a Nijar Kathleen Fitzgubbon da Ministan cikin gida na Nijar Toumba Mohamed

Kafafen gwamnatin Nijar a ranar Talata 26 ga watan Maris sun sanar cewa bayan yi wa juna jaje da barka ta wayar tarho, Janar Abdourahamane Tiani da Vladimir Putin na Rasha, sun tattauna ne kan hanyoyin karfafa huldar kasashen biyu abin da ke kara fayyace kusanci da aka fara samu a tsakaninsu.

Tallafin Amurka ga jamhuriyar Nijar a fannin tsaro wani abu ne da za a kiyasta akan milioyiyin daloli a kowace shekara. Magana ce ta gudunmowar makamai da na’urori da motocin soja, bayanan sirri da horo har da manyan jiragen dakon sojojin samfarin C130 da a yanzu haka ke taimaka wa sha’anin tsaro a Nijar har ma da wasu kasashe makwabtanta.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Amurka Ta Yi Na'am Da Bukatar Kwashe Sojojinta Daga Nijar.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:05 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG