Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Ce Ba Ta Samu Wata Bukata A Hukumance Daga Gwamnatin Mulkin Sojan Nijar Na Ficewar Ta Ba


Celeste Wallander
Celeste Wallander

Wata babban jami’ar ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta shaidawa Majalisar a ranar Alhamis cewa, Amurka ba ta samu wata bukata  a hukumance daga gwamnatin Nijar na ficewa daga kasar ba.

Celeste Wallander, mataimakiyar sakataren tsaro kan harkokin tsaro na kasa da kasa, ta shaidawa kwamitin kula da ayyukan soji na Majalisar cewa, ya zuwa yanzu, gwamnatin mulkin sojan Nijar da aka fi sani da CNSP, ba ta nemi sojojin Amurka da su fice a hukumance ba.

Wallander ta ce, CNSP ya ce matsayin yarjejeniyar dakaru, wanda ya gindaya sharuddan kasancewar sojojin Amurka a wata kasa, yanzu ba shi da amfani. Sai dai, ta ce gwamnatin mulkin sojan ta "tabbatar mana da cewa, sojojin Amurka suna da kariya kuma ba za su dauki matakin da zai jefa su cikin hadari ba."

Abdourahamane Tchiani
Abdourahamane Tchiani

Sojojin Amurka dai na da dakaru kusan 650 da kuma wasu daruruwa masu bayar da tallafi har yanzu a Nijar, wadda a baya ta kasance cibiyar yaki da ta'addanci. Sai dai a watan Yulin da ya gabata wasu sojojin Nijar sun hambarar da zababben shugaban kasar sannan bayan watanni suka nemi sojojin Faransa da su fice daga kasar.

Wallander ta ce Amurka na ci gaba da duba hanyoyin da za a bi wajen gudanar da ayyukan yaki da kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi a yankin.

A jamhuriyar Nijar, ma'aikatan Amurka sun maida dakarunsu a sansani daya, kuma suna ci gaba da gudanar da ayyukan jirage marasa matuki, amma iyakan aikinsu kariya ne kacal, in ji mataimakin sakatariyar yada labarai na Pentagon Sabrina Singh.

"Ana ci gaba da tattaunawa tare da CNSP don a samu hanyar ci gaba," in ji Singh.

Shugaban Rundunar Sojojin Amurka a Afirka Janar Michael Langley, ya ce rashin fahimtar juna ya taka rawar gani sosai a Nijar da ma gwamnatoci da dama da aka yi wa juyin mulki a yankin Sahel a shekarun baya-bayan nan.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG