Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Rasha Ta Aika Sojoji 100 Da Lodin Makamai Wa Nijar


Sojojin kasar Rasha da suka kai makamai Nijar
Sojojin kasar Rasha da suka kai makamai Nijar

Gwamnatin rikon kwaryar jamhuriyar Nijar ta sanar da isowar wasu makamai da na’urorin kare sararin samaniyar da tace sun shigo ne albarkacin huldar ayyukan sojan dake tsakanin Nijar din da Russia.

NIAMEY, NIGER - Tashar talbijan RTN mallakar gwamnati ta gwada wani jirgin da ta ayyana a matsayin wanda ke dauke da lodin makaman da suka iso birnin Yamai tare da sojojin Rasha kimanin 100 da za su yi aikin girka wadanan makamai su kuma bai wa takwarorinsu na kasar horo akan yadda za su yi amfani da su.

Jirgin dakon kaya samfarin ILYUSHIN 76 ne ya sauka filin jirgin saman Yamai a cikin daren Laraba zuwa wayewar Alhamis dauke da makaman kare kai daga hare-haren sama hade da wasu na’urorin kariyar sararin samaniya kamar yadda ake gani a wani rahoton da gidan talbijan mallakar gwamnatin Nijar ya watsa.

‘Yan Nijar dauke da tutotin kasar da na Rasha
‘Yan Nijar dauke da tutotin kasar da na Rasha

Wannan wani bangare ne na sabuwar huldar da hukumomin mulkin soja suka kulla da gwamnatin Vladimir Putin a ci gaba da laluben hanyoyin magance matsalolin tsaron da kasar ke fuskanta. Masani a kan lamuran yankin sahel Dr. Seidik Abba na cewa bai yi mamakin wannan yunkuri na Rasha ba.

Wasu sojojin gwamnatin Rashar a kalla 100 ne aka bayyana cewa sun biyo wadanan kayayyaki da za su jagoranci ayyukan girkawa sannan zasu horar da takwarorinsu na kasar a game da yadda zasu yi amfani da su kamar yadda wani kakakin tawwagar rashawan ya jaddada.

Putin
Putin

Jigo a kungiyar Front Patriotique ta ‘yan goyon bayan hukumomin CNSP Bana Ibrahim na mai alfahari da abinda ya kira sabuwar tafiya.

Sai dai wani dan fafutika Amadou Roufai Laouan Salao na gamayyar COADDE na da shakku kan tasirin wannan hulda tsakanin Rasha da Nijar.

Ayyukan ashan da ake zargin sojan hayar Rasha a kasashen da kamfanin Wagner ke da kwangila abu ne da ya kamata ya zame wa Nijar manuniya inji Souley Oumarou shugaban kungiyar FCR.

Gwamnatin rikon kwaryar Jamhuriyar Nijar ta sanar da isowar wasu makamai da tace sun shigo ne albarkacin huldar tsakanin kasar da Russia.
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:39 0:00

Labarin isowar sojojin horon Rasha hade da kayayyakin kare sararin samaniya na zuwa ne a wani lokacin da ake jiran ganin yadda za ta kaya bayan da hukumomin Nijar suka bukaci Amurka ta kwashe sojojinta 1100 wadanda ke girke a yankin Agadez da sunan yaki da ta’addanci yayinda a Yamai wata kungiyar kin jinin sojojin kasashen ketare ke shirin gudanar da zanga-zanga a gobe Asabar da nufin matsa lamba ga dakarun Amurka su five daga wannan kasa.

A wani matakin kaucewa tafka ta’asa hukumomin birinin Yamai sun sanar da rufe hanyoyin da ke zuwa ofishin jakadancin Amurka daga karfe 7 na safiyar Asabar zuwa 1’30 na rana.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:

Kasar Rasha Ta Aikawa Jamhuriyar Nijar Sojoji 100 Da Lodin Makamai.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG