Gwamnatin Jihar Gombe Ta Kafa Dokar Hana Fita A Billiri

Gidajen da aka kona a zanga zangar garin Billiri

Gidajen da aka kona a zanga zangar garin Billiri

Gwamnatin jihar Gombe, ta kakaba dakor hana fita ta tsawon sa’oi ahirin da hudu (24hrs) a yankin Karamar Hukumar Billiri, daga yau Jumma’a sanadiyar tabarbarewar tsaro bayan da aka fara kone konen wuraren Ibada da gidajen Jama’a da dukiyoyi.

Kwana uku ke nan a jere mata da matasa a masarautar Tangle suka tsare kan babbar hanyar da ta hade jihar Gombe da sauran jihohin Adamawa da Taraba, sabili da batun rikicin zaben sabon Sarkin Tangle.

Gwamnatin jihar Gombe ta ce an gabatar da sunayen mutane uku,da masu zaben sarki suka zabo ga gwamnan sai dai kawo yanzu gwamnan bai fidda sunan wanda aka zaba ba.

Gidajen da aka kona a zanga zangar garin Billiri

Gidajen da aka kona a zanga zangar garin Billiri

A hirar shi da Muryar Amurka, Farfesa Ibrahim Abubakar, sakataren gwamnatin jihar Gombe ya bayyana cewa, masu zaben sarki, bisa al’adar masarautar Tangle su 23 sun fitar da sunayen mutane uku da suka zama fitattu daga cikin masu neman sarautar suka mika ga gwamnan jihar wanda shine ne ke da alhakin zaben mutum daya daga cikin sunayen da aka mika mashi. Sai dai al’ummar Tangle sun sami labarin cewa gwamnan yana niyar zaben wanda ba shine suke so ba, sabili da haka suka fara zanga zangar lumana da nufin nuna rashin amincewarsu da wanda suke tunani gwamnan zai zaba.

Farfesa Abubakar ya ce duk da yake gwamnati ba ta ji dadin rufe hanyoyin da aka yi ba, ta kyale aka ci gaba da zanga zangar lumanar yayinda take tuntuba da neman fahimtar juna. Sai dai a yau jumma’a gwamnati ta sami labarin an fara kona wuraren ibada da gidanjen jama’a, dalili ke nan da ya sa ta kafa dokar hana fita ba dare ba rana don maido doka da oda da kare rayuka da kaddarorin al’umma.

Gidajen da aka kona a zanga zangar garin Billiri

Gidajen da aka kona a zanga zangar garin Billiri

Yace an hana yawo ne domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali kuma da zarar an tabbatar da haka za a dage dokar hana fitan. Sakataren gwamnatin ya musanta rahotannin da ke nuni da cewa, an kama jagororin zanga zangar.

Muryar Amurka ta kuma yi hira da wani mazaunin garin Billiri wanda ya bayyana rashin jin dadi dangane da hukuncin da gwamnati ta dauka na kakaba dokar hana fitan da ya ce rashin fin karfi ne.

A cikin wata rubutacciyar sanarwa da aka rabawa manema labarai, babban ta hannun sakataren kungiyar Lamela Umaru Lakorok, al’ummar Tangle mazauna kasashen ketare ta yi kira ga gwamnan jihar Gome Muhammad Inuwa Yahaya ya sanar da Dr Musa Idris Mai Yamba a matsayin wanda aka zaba ba tare da bata lokaci ba.

Mai Tangale, Dr. Buba Maisharu II wanda shi ne Sarki na 15, ya rasu ne ranar Lahadi 10 ga watan Janairu yana da shekaru 72 a duniya. Basaraken ya rasu ne bayan ya shafe shekaru goma sha tara bisa karagar mulki. A cikin sakonsa yayin sanar da rasuwar basaraken da kuma taya al’ummar masarautar jajen rashin, gwamnan jihar Gomber ya bayyana Mai Tangle Buba Maishanu a matsayin mai kaunar zaman lafiya wanda ya yi aiki tukuru wajen ganin ci gaba, da hadin kai da kuma zaman lafiya a masarautar da kuma yankin baki daya.

Bayan jana’izarsa, bisa ala’ada aka dauki matakin zaben wanda zai gaje shi, sai dai ba a sami cimma matsaya ba sabili da rarrabuwar kawuna.

Saurari rahoton Abdul’wahab Mohammed cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Jihar Gombe Ta Kafa Dokar Hana Fita A Billiri-3:54"