Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Atiku Ya Yi Allah-Wadai Da Kama Masu Zanga Zanga 


Atiku Abubakar
Atiku Abubakar

Tsohon mataimakain shugaban Najeriya kuma dan takarar mukamin shugaban kasa karkashin babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, ya soki matakin kama masu zanga zanga da aka yi.

A cewar Atiku, hakki ne da ya rataya a wuyan jami’an tsaro, su samarwa masu zanga zanga yanayi mai kyau da za su gudanar da zanga zangar lumana kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

“Kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 kamar yadda aka yi masa garanbawul (Shashi na 40) ya ba ‘yan kasa damar su yi zanga zanga cikin lumana, kuma kotu ma ta tabbatar da wannan matsaya. Muna Allah wadai kuma ba za mu lamunta da duk wani mataki da aka dauka da ya sabawa hakan ba.” Atiku ya rubuta a shafinsa na Twitter.

Atiku ya bayyana hakan ne a ranar Asabar - ranar da ‘yan sanda suka yi awon gaba da dumbin masu zanga zanga a kofar Lekki Toll Gate da ke jihar Legas a kudancin Najeriya.

Masu gangamin sun sha alwashin fita su nuna adawarsu kan yunkuri da hukumomi suke yi na sake bude kofar ta Lekki, wacce ta kasance a rufe tun bayan zanga zangar da ta auku a bara wacce ta yi sanadin jikkata mutane da dama.

Mutane da dama ne rahotanni suka ce sun ji rauni bayan da aka zargi jami’an tsaro da bude wuta akan masu zanga zangar neman a rusa rundunar ‘yan sanda ta SARS wacce aka wa lakabi da #Endsars.

Amma jami’an tsaron Najeriya sun musanta wannan ikrari da ke cewa an bude wuta akan masu zanga zangar a ranar 20 ga watan Oktobar bara.

Kwamitin da aka kafa a jihar Legas don gudanar da bincike kan abin da ya faru, ya yanke shawarar sake bude kofar ta Lekki, amma masu zanga zangar sun ce za su fita don nuna adarwasu domin a cewarsu, bude kofar za ta ba da damar a kawar da duk wasu hujjoji da shaida za sun nuna cewa an bude wuta akan mutanen da suka fita zanga zanga a ranar.

Karin bayani akan: Atiku Abubakar, PDP, SARS​, Nigeria, da Najeriya.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG