An haifi sarkin Bi’u Mai Mustapha Umar mai shekaru 50 a duniya, ranar 20, ga watan Yuli, 1970.
Mai Mustapha Umar, wanda shi ne baban dan marigayi sarkin Bi’u Mai Mustapha Aliyu, yayi aiki a mukamai dabam daban da suka hada da na sarauta kafin nada shi Sarki ranar Litinin kwanaki hudu bayan rasuwar mahaifinsa.
Ilimi
Alhaji Mustapha Umar Mustapha ya yi makarantar Firamare a cikin garin Bi’u daga shekarar 1975 zuwa 1981. Bayan kammala makarantar firamare ya tafi makarantar Sakandare ta al’umma mallakar gwamnatin jihar Biu daga shekarar 1983 zuwa 1987.
Mai Mustapha Umar ya tafi karo ilimi a kwalejin koyar da harkokin gudanarwa da nazarin harkokin siyasa dake garin Potiskum daga shekarar 1995 zuwa 1996 inda ya sami takardar diploma a fannin ilimin gudanar da harkokin kananan hukumomi.
Ya kuma sami digiri a fannin ilimin kasuwanci daga jami’ar Maiguri inda ya yi karatu daga shekara ta 2010 zuwa 2015.
Aikin gwamnati.
Bayan samun horo a fannin gudanar da ayyukan kananan hukumomi, Sabon Sarkin Bi’u ya fara aiki a matsayin mataimakin akawu a sashen harkukin kudi na Karamar Hukumar Bi’u a shekarar 1988 inda ya yi aiki na tsawon shekaru kafin a zabe shi dagaci.
Mukaman Sarauta
Sabon Sarkin ya zama dagacin largin Bi’u ta gabas na farko, bayan kirkiro da sabuwar karamar hukumar Bi’u a shekaraar 1999. Aka kuma nada shi Midalan Biu a watan Maris shekara ta 2016.
An nada shi sarkin Bi’u na 29 ranar Talata 22 ga watan Satumba bayan rasuwar mahaifinsa, Mai Mustapha Aliyu wanda ya rasu sakamakon rashin lafiya yana da shekaru 79 a duniya, wanda ya shafe shekaru 31 a karagar mulki.
Masarautar Bi’u
Kananan hukumomin da ke karkashin masarautar mai daraja ta daya sun hada da kananan hukumomin Bi’u, da Bayo da Kusar da kuma Kwaya.
Facebook Forum